Barayi sun harbi wani mutum sannan suka yi masa fashin N1.5m a Bauchi

Barayi sun harbi wani mutum sannan suka yi masa fashin N1.5m a Bauchi

Wasu yan fashi da makami sun kai ma wani mutum hari sannan suka yi masa fashin naira miliyan 1.5 a garin Bauchi.

Lamarin ya afku ne a ranar Jumaúnguwar Wunti kusa da shataletalen babba kasuwa a garin Bauchi.

A tattaro cewa yan fashin su zo ne a kan wata babur sannan suka harbi mutumin yayinda yake tuka motarsa sannan sun waske da naira miliyan 1.5.

An rahoto cewa sun bude wuta domin tsoratar da jama’a su gudu kafin suka harbi mutumin sannan suka gudu da kudin.

A cewar rahotanni, barayin sun yi ta bibiyar mutumin ne daga bankin da ya karbi kudin.

“Baya da suka gama fashin, an rahoto cewa sun doshi hanyar Gombe road ne kafin mutane suka fito uka ceci mutumin da aka yiwa fashi,” inji wani idon shaida.

Sai dai da aka tuntubi kakaki yan sandan jihar Bauchi, DSP Kamal Datti Abubakar, ya bayyana cewa har yanzu ana kan tattara bayanai ka lamarin.

A wani lamari na daban, mu ji cewa rundunar Yansandan jahar Imo ta sanar da cewa wani bom ya tashi a jahar, kuma yayi sanadiyyar mutuwar mutane uku, kamar yadda kaakakin rundunar, Orlando Ikeokwo ya bayyana a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni.

KU KARATA KUMA: Lamarin Almajiranci zai dame mu sosai a nan gaba – Tambuwal

Legit.ng ta ruwaito kaakakin yana cewa lamarin ya faru ne a kauyen Eziorsu dake cikin karamar hukumar Oguta ta jahar Imo, sa’annan ya bayyana sunayen wadanda bom ya tasa kamar haka; Elvis Ukado; Kasiemobi Uzoma da Justice Adie.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel