Latest
Wani magadanci ya yiwa diyarsa gwajin DNA a sirrince. Ya dade yana shakka a kanta don haka yake son kore duk shakkunsa a kanta. Ya tabbata ba shine ubanta ba.
Wani nago ya fasa aure ana tsaka da shagalin aurensa da amaryarsa bayan wani abokinsa ya kyankyasa masa cewa amaryarsa taje yi wa tsohon saurayinta bankwana.
Gabannin babban zaben 2023, jama’a basu fito ba a gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a jihar Filato. Taron ya kasance a bushe ba mutane.
Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa, Yahaya ya roki mazauna jihar su garzaya ofisoshin INEC su karɓo katin zaɓensu kana su dangwalawa APC sak a Zaben 2023.
Shugabannin kungiyar kiristocin Kudancin Kaduna sun ce a ranar 14 ga watan Janairun shekarar 2023 ne za su fada wa mambobinsu wanda za su zaba gwamna a 2023.
Wata budurwa mai halin dattako ta kwace motar da ta ba saurayinta a yayin da suke soyayya bayan shekaru 2 da suka rabu, Ta ga muguwar kazanta cikin motaar.
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana cewa dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar ragargaza sansanonin 'yan bindiga a jihar.
Ma’aikatan gwamnati a jihar Plateau sun shiga yajin aikin gargadi na kwani biyar bayan gwamnati ta ki cika masu wasu bukatunsu ciki da albashin watanni uku.
Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP ya bayyana matsayarsa game da shugabancin PDP da kuma abin da ya sa a gaba. Ya ce ba zai zabi Atiku sai ya ci ka'ida.
Masu zafi
Samu kari