Tinubu vs Osifo: Yadda Zaben Fitar da Dan Takarar Shugaban Kasa na APC ke Gudana a Najeriya

Muhammad Malumfashi avatar Ahmad Yusuf avatar Sharif Lawal avatar
daga Muhammad Malumfashi, Ahmad Yusuf, Sharif Lawal, Abdullahi Abubakar and Sani Hamza
Pinned

Shugaba Tinubu ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen APC a Legas

Shugaba Bola Tinubu ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC da aka gudanar a Ikoyi, Legas.

Shugaban ya yi zaɓen tare da matarsa, Oluremi Tinubu, a mazabarsu yayin gudanar da zaɓen.

A sanarwar da ya fitar a shafinsa na X, Tinubu ya ce dimokuraɗiyya tana bunƙasa ne ta hanyar gudunmawar jama’a, jam’iyyu da cibiyoyi masu ƙarfi.

"APC tana da tsari, kuma ta riga ta kafa rassa a fadin Najeriya. Wasu za su iya haduwa don muradun kansu, amma mun hadu ne da manufa daya, da burin yi wa kasa hidima."

- Shugaba Bola Tinubu.

Shugaban ya ƙara da cewa jam’iyyar za ta ci gaba da ƙarfafa dimokuraɗiyya da kuma gina Najeriya mai ƙarfi ga kowa.

Karanta sanarwar a nan kasa:

All posts
Key Events
Analysis
Exclusive
13 Posts
Sort by
Our live updates have concluded for the day. Catch up on everything you missed below.
Muhammad Malumfashi avatar Ahmad Yusuf avatar Sharif Lawal avatar
daga Muhammad Malumfashi, Ahmad Yusuf, Sharif Lawal, Abdullahi Abubakar and Sani Hamza

Zaben APC: Tinubu Ya Kada Stanley Osifo a Oyigbo

Zaɓen fitar da gwani na Shugaban Ƙasa na APC yana gudana a faɗin jihar Rivers, inda mambobin jam'iyyar a dukkan mazaɓu 319 ke kaɗa ƙuri'unsu domin zaɓar ɗan takarar jam'iyyar a don tunkarar 2027.

Taron ya shaida fitowar dandazon masoya jam'iyya domin zaɓe tsakanin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Stanley Osifo, waɗanda su ne mutum biyu masu neman takarar shugaban ƙasar a APC.

A halin yanzu, mazaɓa ta 3 da ke Oyigbo ta kammala nata zaben, inda aka ayyana Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen, in ji rahoton NTA.

Muhammad Malumfashi avatar Ahmad Yusuf avatar Sharif Lawal avatar
daga Muhammad Malumfashi, Ahmad Yusuf, Sharif Lawal, Abdullahi Abubakar and Sani Hamza

Gwamna Aiyedatiwa Ya Kira Mambobin APC Su Fito Kwansu da Kwarkwata Su Yi Zabe

Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya yi kira ga kowane ɗan jam'iyyar APC da ke faɗin jihar Ondo da ya fito zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa da ake gudanarwa a ranar Asabar, 23 ga Mayu 2026.

Wannan kira nasa yana zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyun siyasa ke gudanar da zaɓukan fidda gwani a faɗin ƙasar nan gabanin babban zaɓen 2027, in ji rahoton Channels TV.

Sanarwar ta bayyana cewa:

“Zuwa ga tabbatattun mambobin babbar jam'iyyarmu, APC, da ke faɗin Jihar Ondo. Yayin da muke shirin zaɓen fitar da gwani na Shugaban Ƙasa, ina kira ga kowane mai rajistar jam'iyyarmu da ya fito kuma ya sa hannu gadan-gadan a cikin wannan muhimmin taron dimokuraɗiyya a mazaɓunsu daban-daban da ke cikin dukkan mazaɓu 203 na Jihar Ondo.
"Ƙarfin jam'iyyarmu ya dogara ne a kan sa hannu kowa, sadaukarwa, da kuma ƙudurin bai-ɗaya na mambobinmu. Wannan zaɓe na fidda gwani yana ba mu wata damar tsara makomar ƙasarmu, sannan mu ƙara ƙarfafa manufofin dimokuraɗiyya da ke haɗa kanmu."
Muhammad Malumfashi avatar Ahmad Yusuf avatar Sharif Lawal avatar
daga Muhammad Malumfashi, Ahmad Yusuf, Sharif Lawal, Abdullahi Abubakar and Sani Hamza

"Ni Ne Babban Jami'in Tattara Sakamako" — Sanwo-Olu kan Zaben APC a Legas

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ziyarci mazaɓar L2, Ikoyi II, da ke jihar, domin sa ido kan yadda ake gudanar da zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na jam'iyyar APC.

A cikin wani bidiyo da mai tallafawa shugaban kasa kan sada zumunta, Olusegun Dada ya wallafa a shafinsa na X, Sanwo-Olu ya shaida wa 'yan jarida cewa:

"Wannan ba mazaɓata ba ce, amma ni ne dai babban jami'in tattara sakamakon zaben, saboda haka dole ne ni ma in duba in ga yadda abubuwa ke gudana a nan. Dukkan shugabannin mazaɓar nan su ma suna nan don ganin yadda abubuwa ke tafiya."

Kalli bidiyon a kasa:

Muhammad Malumfashi avatar Ahmad Yusuf avatar Sharif Lawal avatar
daga Muhammad Malumfashi, Ahmad Yusuf, Sharif Lawal, Abdullahi Abubakar and Sani Hamza

Zaben APC: Gwamna Radda Ya Jaddada Goyon bayansa ga Tinubu

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya halarci zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a mahaifarsa da ke Garin Radda a Ƙaramar Hukumar Charanchi.

Yayin da yake magana da manema labarai a wurin taron, gwamnan ya bayyana ƙaƙƙarfan goyon bayansa ga takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda zai ɗaga tutar jam'iyyar.

Gwamna Radda ya kuma bayyana cewa yadda mambobin jam'iyyar suka yi fitar fari a fadin mazaɓun Katsina ya nuna gagarumin goyon bayansu ga Shugaba Tinubu.

A sanarwar da ofishin sakataren watsa labaran gwamnan ya fitar a Facebook, Dikko Radda ya ce:

"Masu kada kuri'a a APC a fadin jihar Katsina suna goyon bayan Shugaba Tinubu ya zama ɗan takarar jam'iyyarmu a zaben 2027."

Karanta sanarwar a nan kasa:

Muhammad Malumfashi avatar Ahmad Yusuf avatar Sharif Lawal avatar
daga Muhammad Malumfashi, Ahmad Yusuf, Sharif Lawal, Abdullahi Abubakar and Sani Hamza

Zaben APC: Yilwatda Ya Fitar da Sanawar bayan Kada Kuri’arsa

Shugaban jam'iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya fitar da sanarwa a shafinsa na X bayan kada kuri'a, yana mai cewa:

"A yau, na halarci zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na babbar jam'iyyarmu, APC, a mazaɓata ta Ampang ta Gabas da ke ƙaramar hukumar Kanke a jihar Plateau.
"Abin ƙarfafa gwiwa ne ganin yadda mambobin jam'iyya, masu ruwa da tsaki, da wakilai suka fito cikin lumana da sadaukarwa, cike da haɗin kai da yarda da tsarin dimokuraɗiyya na jam'iyyarmu.
"Ina yaba wa dukkan mambobin APC dangane da haɗin kai, da jajircewa da suka nuna a lokacin wannan zaben. A matsayinmu na jam'iyya, za mu ci gaba da ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya na cikin gida, sannan mu gina tubali mai ƙarfi domin ci gaba da daidaiton ƙasarmu gabanin babban zaɓen 2027.
"Cikin haɗin gwiwa, za mu ci gaba da kasancewa masu biyayya ga manufofinmu na yin hidima, haɗa kai, da kuma ci gaban ƙasa."

Karanta sanarwar a nan kasa:

Muhammad Malumfashi avatar Ahmad Yusuf avatar Sharif Lawal avatar
daga Muhammad Malumfashi, Ahmad Yusuf, Sharif Lawal, Abdullahi Abubakar and Sani Hamza

Farfesa Nentawe Yilwatda Ya Bi Layi don Zaben Tinubu a Plateau

Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bi sahun layi domin zaɓen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na jam'iyyar da ke gudana a mazaɓarsa a jihar Plateau.

Imran Muhammad, mai tallafawa shugaban jam'iyyar APC na kasa ta fuskar kafofin sada zumunta, ya wallafa bidiyon zaben a shafinsa na X.

Kalli bidiyon a kasa:

Muhammad Malumfashi avatar Ahmad Yusuf avatar Sharif Lawal avatar
daga Muhammad Malumfashi, Ahmad Yusuf, Sharif Lawal, Abdullahi Abubakar and Sani Hamza

Shugaba Tinubu ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen APC a Legas

Shugaba Bola Tinubu ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC da aka gudanar a Ikoyi, Legas.

Shugaban ya yi zaɓen tare da matarsa, Oluremi Tinubu, a mazabarsu yayin gudanar da zaɓen.

A sanarwar da ya fitar a shafinsa na X, Tinubu ya ce dimokuraɗiyya tana bunƙasa ne ta hanyar gudunmawar jama’a, jam’iyyu da cibiyoyi masu ƙarfi.

"APC tana da tsari, kuma ta riga ta kafa rassa a fadin Najeriya. Wasu za su iya haduwa don muradun kansu, amma mun hadu ne da manufa daya, da burin yi wa kasa hidima."

- Shugaba Bola Tinubu.

Shugaban ya ƙara da cewa jam’iyyar za ta ci gaba da ƙarfafa dimokuraɗiyya da kuma gina Najeriya mai ƙarfi ga kowa.

Karanta sanarwar a nan kasa:

Muhammad Malumfashi avatar Ahmad Yusuf avatar Sharif Lawal avatar
daga Muhammad Malumfashi, Ahmad Yusuf, Sharif Lawal, Abdullahi Abubakar and Sani Hamza

Katsina: Tinubu ya samu kuri'u 18,032 a Ingawa

Sakamakon zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC daga ƙaramar hukumar Ingawa a Jihar Katsina:

Shugaba Tinubu: ƙuri’u 18,032

Stanley Osifo: ƙuri’u 21

Hadimin gwamnan Katsina, MS Ingawa ne ya wallafa sakamakon a shafinsa na X.

Muhammad Malumfashi avatar Ahmad Yusuf avatar Sharif Lawal avatar
daga Muhammad Malumfashi, Ahmad Yusuf, Sharif Lawal, Abdullahi Abubakar and Sani Hamza

Zamfara: Tinubu ya lashe zabe a mazabun Galadima da Kayaye

Sakamakon zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a mazabun Galadima da Kayaye da ke ƙaramar hukumar Talata Mafara, Jihar Zamfara, inda tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata AA Yari, ya kaɗa ƙuri’arsa:

Mazabar Galadima:

Shugaba Tinubu: ƙuri’u 10,678

Stanley Osifo: ƙuri’u 0

Mazabar Kayaye:

Shugaba Tinubu: ƙuri’u 4,897

Stanley Osifo: ƙuri’u 0

Imran Muhammad ya wallafa sakamakon a shafinsa na X.

Muhammad Malumfashi avatar Ahmad Yusuf avatar Sharif Lawal avatar
daga Muhammad Malumfashi, Ahmad Yusuf, Sharif Lawal, Abdullahi Abubakar and Sani Hamza

Tinubu ya lashe zabe a Ute-Okpu Ward 9

Rahoton da Imran Muhammad ya fitar a shafinsa na X ya nuna cewa Shugaba Bola Tinubu ya lallasa Stanley Osifo a zaben fitar da gwani na shugaban kasa da aka gudanar a Ute-Okpu Ward 9, karamar hukumar Ika ta Arewa maso Gabas, jihar Delta.

Har yanzu ana ci gaba da kada kuri'u a zaben da jam'iyyar APC ke gudanarwa a fadin kasar nan.

Muhammad Malumfashi avatar Ahmad Yusuf avatar Sharif Lawal avatar
daga Muhammad Malumfashi, Ahmad Yusuf, Sharif Lawal, Abdullahi Abubakar and Sani Hamza

Zulum ya yi zabe a Borno

Gwamna Babagana Umara Zulum ya hau layi domin zabar Bola Tinubu a zaben fitar da gwani a mazabar Mafa a jihar Borno.

Yawan kuri'un da aka kada:

Tinubu - 2,175

Osifo - 0

Muhammad Malumfashi avatar
daga Muhammad Malumfashi

Gwamnan Kebbi ya hau layin zaben Tinubu

Imran Muhammad wanda hadimin shugaban APC na kasa ne, ya wallafa bidiyon Gwamnan Kebbi, Nasir Idris suna kan layi a wajen zaben tsaida gwani a shafin X.

Gwamnan ya hau kan layi tare da Ministan kasafi, Sanata Atiku Bagudu suka zabi Shugaba Bola Tinubu kuma ya tashi da kuri’u 5, 652 a takarar tsaida gwanin.

Muhammad Malumfashi avatar
daga Muhammad Malumfashi

Tinubu ya isa wurin zabe a Legas

Wani ma’abocin dandalin X mai suna Theo Abu Agada ya nuna bidiyon Mai girma Bola Ahmed Tinubu a makarantar firamaren Ireti a unguwar Ikoyi, jihar Legas.

Shugaban kasar ya tashi daga Abuja domin ya zabi kan shi a zaben tsaida gwani da ake yi a yau.