Duk da Muninta da Kowa ke Gani Har da Mahaifinta, Hamshakin Mai Kudi Yazo Neman Aurenta

Duk da Muninta da Kowa ke Gani Har da Mahaifinta, Hamshakin Mai Kudi Yazo Neman Aurenta

  • Wata mahaifiyar yara bakwai, wacce ta rayu tana mai imani cewa ita mummuna ce, ta bayyana yadda daga karshe ta hadu da mai sonta
  • Matar wacce Kirista ce ta labarta yadda ta taso ne tare da mahaifiyarta bayan mahaifinta yayi watsi dasu tare da cewa ita mummuna ce
  • Wani mutumi ya aureta tana 'yar shekara 15, inda ya rabu da ita gami da sakar mata ragamar yara 3 tana 'yar shekara 22, hakan yasa ta sake wani auren

Tare da kunyata makiya, wata mata mahaifiyar yara bakwai ta dace da soyayyar wani mutumi wanda ba kaunarta kadai yake ba, bai taba cin zarafinta ba balle dukanta kamar yadda ta fuskanta a aurarrakinta na baya.

Addah Doebele daga Busiya cikin kasar Kenya ta fara fafutuka tun tana shekara 12 don tallafawa mahaifiyarta don su yi rayuwa, yayin da mahaifinta yayi watsi dasu.

Kara karanta wannan

Wata Mata Ta Gano Mijinta Ya Yi Amarya a Ɓoye Har Sun Haihu, Ta Je Gidan An Buga Dirama a Bidiyo

Mummuna ce
Duk da Muninta da Kowa ke Gani Har da Mahaifinta, Hamshakin Mai Kudi Yazo Neman Aurenta. Hoto daga YouTube/Afrimax
Asali: UGC

Yayin zantawa da Afrimax, Addah ta bayyana ta taso ne tare da imanin cewa tafi kowa muni, sannan ta matukar shan wahala a aurenta na farko da na biyu wanda ta fuskanci wulakanci da cin zarafi.

A maganganunta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Lokaci bayan lokaci, na kan duba madubi inga kaina, inda nake ganin wata mummunar dabba, wata irin mummunar halitta na kallo na, saboda hakan nayi imani da shi a zuciyata."

Auren Addah na farko

Addah ta bayyana yadda wani mutumi ya mata fyade tana 'yar shekara 15, wanda daga bisani ta zama matarsa ta uku. Sai dai, ta fuskanci cin zarafi da wulakanci daga mutumin da matarsa ta farko.

Tana da shakaru 22, ta fita daga gidan auren tare da yara uku. A cewarta, cin zarafin ya ta'azzara ne. Tsohon mijinta ya sha fada mata ita mummuna ce.

Kara karanta wannan

Budurwa ta Bankado Asalin Mahaifinta, Sirrin da Mahaifiyarta ta Dade tana Boye Mata

Auren Addah na biyu

Daga bisani mahaifiyar yara ukun ta sake auren wani matashi, amma ba da dadewa ba ya fara cin zarafinta shima. Haka zalika, ya kara da fada mata cewa, tayi munin da babu namijin da zai iya aurenta.

Sai dai ta haifi yara hudu dashi

Mahaifiyar yara bakwan ta labarta yadda daga bisani ta fita daga gidan auren shima. Bayan wasu shekaru, a shekarar 2011, ta hadu da wani farar fata gawurtaccen mai hannu da shuni wanda ke matukar kaunarta.

Ba kawai bayyana mata kauna yayi ba, sai da ya aureta. Wanda ya rasu bayan shekaru 10 da aurensu.

Jama'a sun yi martani

Rosalind Pinder tace:

"Wannan irin kyakyawar kaddara. Abun alhini haka nan tayi rayuwar kuruciyarta cikin tsanani. Ubangiji a koda yaushe yana da dalilinsa."

Sally Asantewaa ta ce:

"Kai, wannan kyakyawar kaddara haka. Ubangiji ya cigaba da miki albarka da duk wanda ya karanta wannan. Nagode maka Abba."

Kara karanta wannan

Maa Ta Nadi Bidiyon Mijinta Yana Shan Wankin Kayanta, An Yi Cece-kuce

Marva Sampson ya ce:

"Bata da muni mace ce mai kina, Ubangiji ya cigaba da miki albarka sannan ya tsare miki zuri'ar ki daga Jamaica."

Lady Pink Bags Etc ta ce:

"Wannan shine kusan irin yadda na girma. Kowa na fadamin ni mummuna ce, kuma ba zan taba kai kimar wani abu ba.
Na magance matsalata iya iyawata da kaina. Raunin yayi yawa kuma tabon ya kasa bacewa. Yanzu haka shekaru na 60, ku dauki wani lokaci cikin yini ku yi wa wannan kyakyawar matar addua."

Asali: Legit.ng

Online view pixel