'Ku Taimaka Ku Zabi APC Sak a 2023' Gwamnan Jihar Gombe Ya Roki 'Yan Najeriya

'Ku Taimaka Ku Zabi APC Sak a 2023' Gwamnan Jihar Gombe Ya Roki 'Yan Najeriya

  • Gwamnan Gombe ya roki mazauna jihar su taimaka su zabi jam'iyyar APC tun daga sama har ƙasa a 2023
  • Gwamnan ya ci gaba da yawon tallata kudirin zarcewa a kujerarsa, ya shiga yankunan karamar hukumar Balanga
  • Kodinetan kamfen APC a jihar, Jamil Gwamna, ya ce jam'iyyar PDP ba zata kai labari ba domin ba ta tsinana komai ba

Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya roki magoya baya su garzaya su karɓi Katin zabensu domin samun damar kaɗa wa APC kuri'unsu a 2023.

Gwamnan yace ɗumbin ayyukan da ya zuba a mulkinsa na farko babban alama ce dake nuna dacewarsa musamman yadda ya maida hankali wajen yaye matsin da mutane ke ciki.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya.
'Ku Taimaka Ku Zabi APC Sak a 2023' Gwamnan Jihar Gombe Ya Roki 'Yan Najeriya Hoto: Inuwa Yahaya
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta tattaro cewa Inuwa Yahaya ya yi wannan jawabin ne yayin kamfe a gundumomi 5 da suka haɗa ƙaramar hukumar Balanga ta arewa ranar Litinin.

Kara karanta wannan

2023: Insha Allahu 'Yan Najeriya Ba Zasu Yi Dana Sani Ba Idan Na Zama Shugaban Kasa, Tinubu

Da farko, gwamnan ya ziyarci fadar Bala Waja, babban Basarake a ƙaramar hukumar, Muhammad Danjuma, domin sanar da shi sun zo kamfe a yankin Masarautarsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ɗanjuma ya shaida wa gwamnan cewa ya kwantar da hankalinsa, zai samu kuri'u tuli sakamakon romon ayyukan da ya zuba wa al'umma kamar, "Gina hanyoyi, ɗaukar ma'aikata."

A cewar Basaraken, "Yayin ɗaukar malaman makaranta na kwanan nan, Balanga ce ta zo na biyu cikin jerin waɗanda suka fi amfana."

Gwamna Yahaya ya roki mazauna jiharsa

Yayin ziyarar da ya kai wasu gundumomi, gwamna Yahaya ya roki mutane su karɓo katin zaɓensu, "Domin haka ne kaɗai zai basu damar zaben APC a kowane matakin gwamnati a 2023."

Ya roki mazauna jiharsa ta Gombe su taimaka su zabi jam'iyyar APC sak tun daga sama har ƙasa idan zaɓe ya zo.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Fara Ƙalaman Nuna Wanda Zai Mara Wa Baya Tsakanin Atiku da Tinubu a 2023

PDP ba zasu kai labari ba - Jamil Gwamna

Da yake nasa jawabin, kodinetan kwamitin yakin neman zaɓen APC a Gombe, Jamil Gwamna, yace PDP zata sha kaye saboda ba abinda ta tsinana wa al'umma a baya.

Gwamna ya yi kira ga masu katin zaɓen su jefa wa APC kuri'unsu tun daga sama har ƙasa domin baiwa gwamnati damar ci gaba da ayyukan da ta ɗauko a zangon farko.

A wani labarin kuma Shugaban APC na kasa yace Bola Tinubu ne zai zama magajin shugaba Buhari a babban zaɓen 2023

Sanata Abdullahi Adamu ya sanar da hakan ne a garin Kaduna yayin gangamin ralin jam'iyyar APC na farko a shiyyar arewa maso yamma.

Shugaban APC ya ƙara da cewa ganin tururuwar da jama'a suka yi a Filin wasan Ahmadu Bello dake Kaduna kaɗai ya isa alama, ya gode wa mahalarta gangamun daga jihohi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel