2023: Atiku Ya Hadu Da Gagarumin Cikas Yayin da Mutane Suka Ki Fitowa Gangamin Kamfen Din PDP a Filato

2023: Atiku Ya Hadu Da Gagarumin Cikas Yayin da Mutane Suka Ki Fitowa Gangamin Kamfen Din PDP a Filato

  • Rikicincikin gida da ya dabaibaye PDP ya yiwa jam’iyyar cin kazar kuku domin alamu sun nuna hakan a gangaminta na baya-bayan nan
  • Hakan ya kasance ne yayin da mutane suka ki fitowa a gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar da aka yi a filin wasa na Rwang Pam
  • Abun mamaki, a watan da ya gabata, Bola Tinubu ya kaddamar da kamfen dinsa a wannan filin wasan kuma ya cika fam da mutane

Plateau - Wani rahoton The Nation ta rahoto cewa mutane basu fito ba sosai a wajen yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) da ya gudana a filin wasa na garin Rwang Pam a Jos, babban birnin jihar Filato.

Rumfuna da dama a wajen gangamin sun kasance a bushe wayam babu mutane har zuwa karfe 1:00pm a gangamin da aka shirya yi 10:00 na safe.

Kara karanta wannan

Dan Ba Kara Zaben APC A 2023: Mun Zabi Buhari Wahala Ta Kusan Kashe Mu, iInji 'Yan Arewa

Atiku da mutanensa
2023: Atiku Ya Hadu Da Gagarumin Cikas Yayin da Mutane Suka Ki Fitowa Gangamin Kamfen Din PDP a Filato Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Wai me ke faruwa ne?

Koda dai an shirya munbarin da wuri, magoya bayan jam'iyyar da dama da mazauna sun kauracewa wajen.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai kuma, an gano masu biyayya ga jam'iyyar a filin wasan suna jiran isowar dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar.

The Nation ta rahoto cewa yan tsirarun mutane da suka hallara sun fara mamaye wajen da misalin 11:00 na safe.

Gangamin yakin neman zaben PDP da gangamin kamfen din APC

An tattaro cewa manyan otel-otel da masaukin baki a Jos sun cika makil da mutane.

Da misalin karfe 1:00 na rana, filin wasan mai cin mutum 45,000 bai cika ba.

Yawan mutanen da suka hallara a filin wasan basu da yawa idan aka kwatanta da abun da ya faru lokacin da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasarta.

Kara karanta wannan

Emefiele zai kashe mu: Jam’iyyun Siyasa Sun Yi Wayyo da Dokar Takaita Cire Kudi

Bidiyo ya bayyana

An wallafa wani bidiyon gangamin a shafin jam'iyyar na Facebook.

Wike da Ortom sun kauracewa haduwa da Atiku a filin jirgi

A wani labarin, mun ji cewa Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue da Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas sun kauracewa haduwarsu da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP.

Ortom dai ya je tarar Wike ne inda suka ci karo da yan tafiya gangamin yakin neman zaben PDP a jihar Nasarawa bayan sun yada zango a Benue, a lokacin kuma saura minti biyar Atiku ya sauka daga jirgi amma suka kada kai suka yi tafiyarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel