2023: Jigon APC Mai Ƙarfin Faɗa A Ji Ya Bayyana Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Da Ke Tayar Wa Tinubu Hankali

2023: Jigon APC Mai Ƙarfin Faɗa A Ji Ya Bayyana Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Da Ke Tayar Wa Tinubu Hankali

  • Osita Okechukwu, babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya fasa kwai
  • Ya bayyana cewa babban barazana ga takarar shugaban kasar Bola Tinubu shine takwararsa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi
  • Okechukwu ya ce hasashen da ake yi na cewa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP barazana ga Tinubu ne ba gaskiya bane

An bayyana Peter Obi da Labour Party a matsayin babban dan takara da zai iya fita na fito a zaben shugaban kasa na 2023 da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu.

Osita Okechukwu, fitaccen jigon jam'iyyar mai mulki na kasa ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin hira da ya yi a shirin The Morning Show na Arise TV.

Bola Tinubu
2023: Jigon APC Mai Karfin Fada a Ji Ya Bayyana Dan Takarar Shugaban Kasa da Ke Tayar Wa Tinubu Hankali. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Daukarwa Matasa Da Mata Wani Babban Alkawari Idan Ya Gaje Buhari

Osita, wanda kuma shine direkta janar na muryar Najeriya, VON, ya yi watsi da cewa Atiku Abubakar na PDP ne babban barazana ga jam'iyyar mai mulki.

Ya ce:

"Mun fi damuwa da Peter Obi da saura. Kwankwaso kwarare ne kuma ya cacanta, amma akwai kalubalen yanki a kansa. Don haka, idan ka ce mana Peter Obi, za mu iya cewa eh, a nan ne muke damuwa," amma ba Atiku wanda ya rasa magoya bayansa ba.
"Atiku ba zai iya yin nasara ba; ina kallubalantar masu cewa hakan. Ba zai ya samun kuri'u miliyan 12 na Buhari ba; Ba shi da irin kuri'un da Buhari ke da shi."

Okechukwu ya yi watsi da damar Atiku

Kamar yadda Daily Independent ta rahoto, ya kafa hujjarsa da cewa Atiku ya rasa manyan magoya bayansa.

Kazalika, Okechukwu ya ec Tinubu yana da abin da ake bukata don zama shugaban kasa na gaba kuma abin da ya aikata a baya ya isa ya zama masa hujja.

Kara karanta wannan

Ta Ya Ka Tara Dukiyarka Idan Gidanku Talakawa Ne? Atiku Ya Aika Sako Ga Tinubu

Ya ce:

"Shi kuma Asiwaju Bola Tinubu, abin da babu wanda zai musanta shine ya iya alonsa. Yana da kwarjini, ya san kasar nan, kuma ya dade yana shiri. Kuma ba mu damu da PDP ba; misali, Atiku ya rasa tushen magoya bayansa."

Zaben 2023: Bola Tinubu ya ci zabe ya gama, Tsohon dan takarar gwamna na Filato

A wani rahoto, David Victor Dimka, tsohon dan takarar gwamnan jihar Filato karkashin jam'iyyar APC, ya yi hasashen cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne zai yi nasara a babban zaben 2023.

Dimka, tsohon kwanturola janar na hukumar kwastam, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Jos, babban birnin jihar Filato.

Asali: Legit.ng

Online view pixel