Magidanci Ya Baiwa Matarsa Sakamakon Gwajin DNA Da Ke Nuna Diyarsu Ba Shi Ya Haifeta Ba, Bidiyon Ya Yadu

Magidanci Ya Baiwa Matarsa Sakamakon Gwajin DNA Da Ke Nuna Diyarsu Ba Shi Ya Haifeta Ba, Bidiyon Ya Yadu

  • Bayan ya gudanar da gwajin kwayoyin halitta, magidanci ya shiga damuwa bayan ya gano ba shine uban diyarsu ba
  • Ya hada sakamakon gwajin a wata takarda sannan ya mikawa matarsa wacce ta shiga kaduwa ganin cewa ya bankado sirrinta
  • A cewar mutumin, ya ce ya fara samun shakku kan kasancewarsa mahaifin yarinyar bayan ya lura da wasu yan abubuwa

Wani magidanci ya gano cewa matarsa na cin amanarsa da wani daban da taimakon gwajin kwayoyin halitta wato DNA.

A wani bidiyon TikTok da ya yadu, mutumin ya isa ga matarsa a madafi sannan ya gabatar mata da sakamakon gwajin.

Matar aure
Magidanci Ya Baiwa Matarsa Sakamakon Gwajin DNA Da Ke Nuna Diyarsu Ba Shi Ya Haifeta Ba, Bidiyon Ya Yadu Hoto: TikTok/@arianaxinxin
Asali: UGC

Ta yi kokarin bude takardar cike da murna tana mamakin ko wani tikitin zuwa shakatawa ne ko wani abu makamancin haka.

Sai ya sanar da ita cewa sakamakon gwajin DNA ne da ya yi a sirrince wanda ke nuna cewa diyarsa ba shine ubanta ba.

Kara karanta wannan

A Ranar Aure, Ango ya Fasa Bayan Gano Amarya ta Kaiwa Tsohon Saurayinta Ziyarar Bankwana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutumin ya ce yana ta shakku a kan yarinyar kuma hakan yasa shi yin gwajin. Ya bayyana cewa yanzu ya san abun da take boye masa.

Da take martani, kawai matar ta nuna fushinta kan dalilinsa na kawo irin wannan labari a daidai wannan lokaci.

Kalli bidiyoyin a kasa:

Jama'a sun yi martani

Dee Lashaun ta ce:

"Batun rashin yarda ya kunno ka. gaskiya ba zan ce na ga laifinsa ba saboda zarginsa ya zama gaskiya."

Harvey Donovan ta ce:

"Idan ba shirin kwaikwayo bane, dan Allah fada mun yadda ya samu samfirin jini daga wajenta ba tare da an lura ba."

shygirluvalle ta ce:

"Ta so a lallashe ta kowani uba yana da yancin sanin gaskiya."

Saurayi ya gano budurwarsa na cin amanarsa da taimakon GB Whatsapp

A wani labarin, asirin wata budurwa ya tonu yayin da saurayinta ya gano cewa tana ci masa amana da wani da taimakon dandalin zumunta na GB Whatsapp.

Kara karanta wannan

Bidiyon Cikin Dankareren Gidan Da Wani Matashi Ya Kerawa Kansa, Ya Ji Kayan Alatu Kamar Fadar Sarki

Tun farko dai budurwar na da wani saurayi na daban da suke sharholiya don haka ta tsantsara masa sako na musamman a ranar zagayowar ranar haihuwarsa amma sai ta taki rashin sa'a ta turawa dayan saurayin nata.

Ta share sakon amma abun ya ki gogewa a bangaren wancan saurayin domin dai GB Whatsapp ne da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel