Hazikin Yaro Mai A 7 a WAEC Yana Zaune Gida Dirshan Saboda Rashin Kudin Cigaba da Karatu

Hazikin Yaro Mai A 7 a WAEC Yana Zaune Gida Dirshan Saboda Rashin Kudin Cigaba da Karatu

  • Tagab Mathew, wani yaro ne mai matukar hazaka da ya ci 7As a jarabawar kammala sakandare gami da samun jimillar takardu shida a BECE
  • Duk da irin bajinta da hazakarsa, alamu na nuna mafarkinsa na zama injiiniya ba zai zama gaskiya ba saboda rashin wanda zai dauki dawainiyarsa
  • Mutane da dama sun yi tsokaci game da halin da Mathew ke ciki bayan nuna kwazon da yayi wanda hakan ya karade kafafan sada zumuntar zamani

Bayan lashe jarabawarsa ta kammala sakandare (WASSCE) tare da cin takardu 7 da mataki mafi daraja(7As) a shekarar 2022, alamu na nuna cewa matashin zai dakata da burinsa na cigaba da karatu.

Tagab Mathew ya karanci kimiyya a sakandare sannan yayi nasarar lashe takardu bakwai da maki mafi yawa wadanda suka hada da; Social Studies, Core Mathematics, Integrated Science, Elective Mathematics, Biology, Chemistry, Physics, da Taren turanci.

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Jigo a Najeriya ya fusata kan kin hukunta wadanda suka kashe Deborah

Yaro mai hazaka
Hazikin Yaro Mai A 7 a WAEC Yana Zaune Gida Dirshan Saboda Rashin Kudin Cigaba da Karatu. Hoto daga @manaaf
Asali: UGC

Duk da irin bajintar da ya nuna, dole tasa ya dakata da burinsa na zama injiniya tare da cigaba da aikinsa na kere-kere saboda rashin wanda zai dauki dawainiyarsa.

Wani mai amfani da yanar gizo ya bayyana halin da Mathew ke ciki a wata wallafar da yayi a Twitter wanda Legit.ng ta binciko.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai amfani da kafar sada zumuntar @Manaaf- official ya bayyana yadda matashin ba zai samu damar haurawa matakin jami'a ba saboda rashin wanda zai dauki ragamar karatunsa.

"Abun takaici! Tagab Mathew, wanda ya lashe jarabawar kammala sakandare da jimillar maki shida a BECE sannan ya samu maki mafi yawa a takardu bakwai na WASSCE.
Bashi da wani zabi da ya wuce ya cigaba da zama a gida tare da cigaba da 'yar buga-bugarsa duba da mafarkinsa na zama injiniya ya tsaya cak saboda rashin wanda zai dauki dawainiyar karatunsa na jami'a!! A taimaka,"

Kara karanta wannan

Majalisar 'Dinkin Duniya Ta Bukaci Gwamnatin Da Ta Binciki Zargin Zubar Da Ciki Da Sojoji Ke Tilastawa Mata

- A cewarsa.

Jama'a sun yi martani

Mutane da dama sun garzaya sashin tsokaci don tofa albarkacin bakunansu karkashin wallafar, wacce ta tattara mutane 1,338 da suka sake wallafar, masu kari da fashin baki gami da sake wallafar 51, da jinjina 1,958 daga lokacin da aka tattara wannan rahoton.

Masu amfani da yanar gizo sun bayyana ra'ayoyi daban-daban game da halin da Tagab Mathew ke ciki.

@sirhbryte ya ce:

"Meyasa? Ba zai iya bin manhajar dake bada bashi ga dalibai ba https://sltf.gov.gh? Abun da kawai yake bukata shi ne katin Ghana."

@OtuSowah ya ce:

"Iyaye sun tara kudi isashshe don daukar nauyin karatun 'ya'yansu zuwa matakin gaba da sakandare saboda FSHS. 'Dan da iyayensa ba zasu iya daukar nauyin karatunsa ba a matakin sakandare zasu iya a matakin gaba da sakandare, haka dai gwamnati ke cewa."

@nambepatrick yayi tsokaci:

"St. James diie, abun yayi tsanani, dan uwana ya ci 6As, B3 a turanci da B2 a social studies. Yanzu kudi ne matsalar. Ko ina ana kukan babu."

Kara karanta wannan

Duk da Kyauna, “Samarin Shaho” Guduna Suke yi, Budurwa Mai Kamun Kai Tayi Bayani

@PromzyKingaton yayi martani:

"maimakon koyin kere-kere da yake, ai da yayi amfani da fasahar wajen neman tallafin karatunsa. Katin cire kudi na daliban da suke zauni gida bayan kammala karatu yana nan. GNPC ma yana nan. Buga-bugar ba mafita bace idan dai yanason cigaba da karatunsa."

@EFaruk14 yayi wallafa:

"Da sannu taimako zai riskesa idan ba yanzu ba nan gaba kadan. Amma a yanzu, wadanda suke da manyan kamfanonin kere-kere zasu iya daukansa a matsayin mai koyo na wucin gadi, gami da biyansa dan wani abu duk wata, tare da horar da shi yadda zai dunga tara kudin. Bayan shekara zai iya sake neman cigaba da karatu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel