Bayan Ango Ya Gano Amarya Ta Kai Ziyarar Bankwana ga Tsohon Saurayinta, Ya Fasa Auren

Bayan Ango Ya Gano Amarya Ta Kai Ziyarar Bankwana ga Tsohon Saurayinta, Ya Fasa Auren

  • Wani mutum ya fasa auren amaryarsa a ranar bikinsu bayan gano amaryar taa kaiwa tsohon saurayinta ziyarar bankwana
  • A wani bidiyo da yayi yawo, an ga amaryar na rokon mutumin da titi inda ta dasa guiwoyinya a kasa, amma ya ki saurararta
  • Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin masu amfani da yanar gizo, wadanda suke ta tofa albarkacin bakunansu karkashin bidiyon da aka wallafa

Wasu ma'aurata, wadanda aka boye sunansu sun karade kafafan sada zumuntar zamani bayan ango ya fasa auren amaryarsa a ranar shagalin bikin.

Angel FM's Opanyin Darko, wanda ya labarta yadda lamarin ya auku daga Kasoa, Ghana, ya bayyana yadda mutumin ya gano amaryarsa na cin amanarsa a karon na karshe kafin bikin.

Ango ya fasa aure
Bayan Ango Ya Gano Amarya Ta Kai Ziyarar Bankwana ga Tsohon Saurayinta, Ya Fasa Auren. Hoto daga @officialnanaquame
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Ki Rufa min Asiri: Fasto Ya Marairaice Yana Roko Budurwa Kada ta Fitar da Bidiyon Sharholiyarsa

An ruwaito yadda labari ya riski angon, wanda wani abokinsa ya sanar masa, hakan yasa angon ya tada batun ana tsaka da shagalin bikin aurensu.

A bidiyon da ke yawo, an ga yadda amaryar cikin shigar amare gami da kayatarwa take kuka da guiwoyinta biyo a kasa tana rokon mutumin da ya mata afuwa amma yayi kunnen uwar shegu.

Tsokacin 'yan kasar Ghana game da bidiyon

Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinau bayan fitar bidiyon mara dadi da soshiyal mediya.

Ga wasu daga cikin tsokacin jama'a da Legit.ng ta tattara:

Irene Yeboah ta ce:

"Idan da ni ne shi ba zan bata lokaci na wajen zuwa haduwa da wani shedani ba... Kawai zan jira ta a wajen shagalin biki mu kwashi rawarmu."

Albert Nana okyere ta ce:

"Wannan abu yayi tsanani, na san wani wanda ya kwanta da budurwa ana saura mako daya bikinta tare da asalin wanda za ta aura, saboda haka tana iya yuwuwa."

Kara karanta wannan

Saurayi Ya Haɗu Da Sahibarsa Baturiya Bayan Shekara 2 Suna Soyayya A Intanet, Bidiyonsu Ya Sosa Zuciyar Mutane

Frankjoe ya ce:

"Ina mamakin taya wasu ke tunani? Za ki yi aure amma kina kaiwa tsohon saurayinki ziyara."

Ango ya fasa aure ana dab da daurawa

A wani labari na daban, wani ango ya tashi hankalin jama'ar da suka halarci shagalin aurensu har da amaryarsa.

Ango ya bankado cewa amaryarsa tana da 'ya'ya har biyu amma ta boye masa bata sanar masa da hakan ba ko da wasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel