Ana tsaka da Yakin Iran da Amurka, Pakistan Ta Kai Mummunan Hari a Afghanistan

Ana tsaka da Yakin Iran da Amurka, Pakistan Ta Kai Mummunan Hari a Afghanistan

  • Akalla mutane 13 ne suka mutu yayin da Pakistan ta kai sababbin hare-haren sama a lardunan kasar Afghanistan
  • Kakakin Taliban, Zabihullah Mujahid, ya ce yara 11, mace guda da dattijo daya ne suka rasa rayukansu, yayin da mutum 14 suka jikkata
  • Hare-haren sun biyo bayan harin da ake zargin 'yan Taliban na Pakistan sun kai kan wani wurin tsaro a Khyber Pakhtunkhwa, inda jami'ai shida suka mutu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kabul, Afghanistan - Kasar Afghanistan ta sanar a ranar Laraba 10 ga watan Yunin 2026 cewa Pakistan ta kai sababbin hare-haren sama a cikin kasar.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa lamarin ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 13 tare da jikkata wasu 14.

Pakistan ta kai hari a Afghanistan
Firayim ministan Pakistan, da jagoran addini a Afghanistan, Mullah Hibatullah Akhundzada. Hoto: Tingshu Wangi - Pool, Rob Welham/Universal History Archive.
Source: Getty Images

Kasashen biyu sun shafe watanni suna musayar hare-hare a kan iyaka, rikicin da ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane tun bayan barkewarsa, cewar AP News.

Kara karanta wannan

Dubun wasu rikakkun 'yan fashi da makami ta cika a jihar Adamawa

Pakistan ta kai hari a lardunan Afghanistan

Babban kakakin Taliban, Zabihullah Mujahid, ya ce hare-haren na baya-bayan nan sun auka kan lardunan Khost, Kunar da Paktika da ke Afghanistan.

A cewarsa, yara 11 ne suka mutu a hare-haren, tare da mace guda da kuma wani dattijo daya, abin da ya kara dagula halin tsaro.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, Gwamnatin Pakistan ba ta fitar da wata sanarwa da ta tabbatar ko ta musanta kai hare-haren ba.

Hare-haren sun zo ne kwana guda bayan wasu da ake zargin 'yan Taliban na Pakistan ne suka kai hari kan wani wurin tsaro.

An kai harin ne a yankin Hasan Khel da ke Arewa maso yammacin lardin Khyber Pakhtunkhwa, kusa da iyakar Afghanistan da Pakistan.

An hallaka mutane da dama a harin Pakistan a Afghanistan
Firaministan kasar Pakistan, Muhammad Shahbaz Sharif lokacin da yake jawabi a taron zuba jari na FII a Saudiyya Hoto: Fayez Nureldine.
Source: Getty Images

Nasarar da aka samu kan mahara a Pakistan

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Pakistan ta ce an kashe jami'ai shida na rundunar 'Federal Constabulary' a mummunan musayar wuta da ta biyo baya.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta harbo jirgin yakin Amurka, Trump ya sha alwashin ɗaukar fansa

Rahotanni daga hukumomin yankin sun ce jami'an tsaro sun kashe mutum takwas daga cikin maharan tare da dakile yunkurinsu na kwace sansanin.

Daga baya, Ministan harkokin cikin gida na Pakistan, Mohsin Naqvi, ya halarci sallar jana'izar jami'an da suka mutu a birnin Peshawar.

Naqvi ya yaba wa sadaukarwar jami'an da suka rasa rayukansu tare da jajanta wa iyalansu kan wannan babban rashi da suka yi, cewar Arab News.

Ya kuma jaddada cewa Pakistan za ta ci gaba da hada kai wajen yaki da masu tayar da kayar baya da kuma kara tsaurara matakan tsaro.

Tun daga karshen watan Fabrairu, Pakistan da Afghanistan ke ci gaba da artabu bayan Afghanistan ta kai farmaki a matsayin ramuwar gayya ga hare-haren Pakistan a cikin kasarta.

Pakistan ta magantu kan sulhunta Iran, Amurka

A baya, an ji cewa Pakistan ta ce za ta karɓi bakuncin tattaunawa tsakanin Amurka da Iran kan rikicin da ke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ana ci gaba da tattaunawa kuma suna tafiya yadda ya kamata duk da yana kara shirin yaki.

Iran ta yi barazanar kai hari kan sojojin Amurka da abokan hulɗarsu a yankin matuƙar ana ci gaba da kai mata farmaki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.