Dole Ayu Ya Sauka Amma Banda Matsala Da Atiku, Gwamna Wike

Dole Ayu Ya Sauka Amma Banda Matsala Da Atiku, Gwamna Wike

  • Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, yace ba shi da wata rigima ta kai da kai tsakaninsa da Atiku Abubakar
  • Wike, jagoran G5, ya jaddada cewa bukatarsa kawai arewa ta hakura ta miƙa wa ɗan kudu shugabancin jam'iyyar PDP
  • Gwamnan wanda ya sha ƙasa hannun Atiku a zaben fidda gwanin PDP ya yi ikirarin arewa na neman mamaye komai

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike, yace banda bukatar arewa ta hakura da kujerar shugaban PDP ta baiwa kudu, ba shi da wata matsala ta karan kai tsakaninsa da Atiku Abubakar.

Wike ya faɗi haka ne yayin da ya karɓi bakuncin 'yan siyasa da majalisar Dattawan Ribas ƙarƙashin jagorancin Chief Ferdinand Alabraba r ranar cikarsa shekara 55 a gidansa dake Rumueprikom.

Wike da Atiku.
Dole Ayu Ya Sauka Amma Banda Matsala Da Atiku, Gwamna Wike Hoto: vanguard
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa gwamnan ya ƙara da cewa ko kaɗan bai yi nadamar neman takara a zaben fidda ɗan takarar shugaban kasa ba, wanda ya sha kaye hannun Atiku.

Kara karanta wannan

"Ku Taimaka Ku Zabi APC Sak a 2023" Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Roki 'Yan Najeriya

A kalamansa da The Nation ta rahoto Wike yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ban yi dana sanin shiga tseren neman tikitin shugaban kasa ba, da sunan Allah, ina mai farin cikin sanya jihar Ribas alfahari, a iya yanda nake tunani. Da sun bari an yi abinda ya dace da ni zan lashe zaɓen amma ba komai, ta faru."
"Wasu na cewa ai saboda na sha kaye ne a zabe, Ni bai dame ni ba domin ban yi rashin nasara ba. Wannan shi ne karon farko da na nemi takarar Mulkin Najeriya kuma mun yi tasiri."
"Idan suna ganin abune mai sauki su jaraba. Bani da matsala da ɗan takarar shugaban kasa (Atiku), abinda na ce me mutanen Ribas suke ƙauna? Me mutanen kudu maso kudu da kudancin Najeriya zasu amfana?"

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa har yanzun PDP na cikin rigingimu tun bayan samun saɓani da tsagin gwamna Wike, wanda ya haɗa gwamnonin jam'iyyar 5.

Kara karanta wannan

2023: Insha Allahu 'Yan Najeriya Ba Zasu Yi Dana Sani Ba Idan Na Zama Shugaban Kasa, Tinubu

Insha Allahu 'Yan Najeriya Ba Zasu Yi Dana Sani Ba Idan Na Zama Shugaban Kasa, Tinubu

A wani labarin kuma Bola Ahmed Tinubu ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa Insha Allahu ba zasu yi dana sanin zaɓensa ba a 2023

Da yake jawabi a gangamin APC na Kaduna, ɗan takarar shugaban kasan yace zai magance matsalar 'yan bindiga idan Allah ba shi mulkin Najeriya.

Tsohon gwamnan jihar Legas ɗin ya ba mutane mamaki yadda daga zuwa Kaduna ya wuce Birnin Gwari kuma yayin dawowarsa yamma ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel