Ba Zan Zabi Atiku Ba Sai an Ba Yarbawa Shugabancin PDP, Inji Tsohon Mataimakin Shugaban PDP, Bode George

Ba Zan Zabi Atiku Ba Sai an Ba Yarbawa Shugabancin PDP, Inji Tsohon Mataimakin Shugaban PDP, Bode George

  • Jigo kuma dattijon jam’iyyar PDP ya bayyana matsayarsa game da zaban Atiku a zaben 2023 mai zuwa nan da badi
  • Bode George ya ce ba zai zabi Atiku har sai an dauki kujerar shugabancin PDP an kai ta yankin Kudu maso Yamma
  • Gwamnonin G-5 na ci gaba da nuna adawa da shugabancin PDP, sun ce ba za su yiwa Atiku kamfen sai ya cika burinsu

Najeriya - Dattijon kasa kuma jigon PDP y ace ba zai zabi Atiku a zaben 2023 har sai jam’iyyar ta dauki shugabanta ta kai yankin Kudu maso Yammacin kasar nan.

Bode George, wanda tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP ne bayyana hakan ne a yayin wata tattauna da gidan talabijin na Arise News a ranar Talata, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ta karewa Tinubu a Arewa, Atiku ya karbi mambobin APC 10,000 zuwa APC a jihar Arewa

Jigon na PDP dai na daga cikin masu kira da kwace kujerar shugaban PDP na kasa mai ci Iyorchia Ayu tare da nada sabon shugaban jam’iyyar a matakin kasa.

Bode George ya ce ba zai zabi Atiku ba
Ba Zan Zabi Atiku Ba Sai an Ba Yarbawa Shugabancin PDP, Inji Tsohon Mataimakin Shugaban PDP, Bode George | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Kira ga kwace kujerar Ayu ya faro ne daga yadda aka ba Arewacin Najeriya tikitin takarar shugaban kasa tare da ba yankin shugabancin jam’iyya, lamarin da ya jawo tsaikon cikin gida ga PDP, Ripples Nigeria ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A aje komai a mazauninsa, a kwace kujerar Ayu a ba Kudu maso Yamma

Da yake tsokaci game da lamarin, Bode ya ce rikicin PDP mai sauki ne a warware shi matukar aka dauki komai a kai shi ga mazauninsa yadda ya dace.

Ya kuma kara da cewa, yankin Kudu maso Yamma bai da wata kujera mai girma a matakin kasa, musamman shugabancinta na kasa tun bayan kafa fta, don haka dole a gyara kafin zaben 2023.

Kara karanta wannan

2023: Jigon dattijon PDP ya caccaki Atiku, ya ce gwamnonin G-5 dole su yi adawa dashi

Saboda haka ne Bode ya ce ba zai zabi Atiku ba har sai an gyara wannan rikicin cikin gida, kuma an daidaita shugabancin jam’iyyar kamar yadda muradin ‘yan Kudu ya nema.

Gwamnonin G-5 masu adawa da tafiyar Atiku da shugabacin Ayu

Baya ga wannan, akwai wasu jiga-jigan gwamnoni 5 da suka kira kansu da ‘G-5’ da ke adawa da takarar Atiku da kuma shugabancin jam’iyyar PDP.

Sun bayyana abin da suke son cimmawa, muradin mai kama da na Bode Goerge da ke neman ganin karshen kujerar shugabancin PDP daga hannun Ayu.

Da yake yaba su, Bode Goerge ya ce sam babu wani abu da zai iya raba kan wadannan jiga-jigan gwamnoni kuma ba za su yiwa Atiku kamfen ba a zaben 2023 sai har ya cika burinsu.

Tinubu ba dan jihar Legas bane, inji Bode George

A hirar dai da aka yi dashi, Bode Goerge ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ba dan asalin jihar Legas bane.

Kara karanta wannan

Kowa ya huta: Atiku ya fadi yadda zai yi kungiyar ASUU idan ya gaji Buhari a zaben 2023

Ya ce, ya zuwa yanzu dai Tinubu ya gaza gamsar da Duniya cewa shi dan asalin jihar Legas ne ko kuma tsatsonsa na yankin ne.

Tun farko dama akwai ‘yar tsama tsakanin Bode George da Bola Tinubu, kuma yakan yi maganganu irin wadannan duk sadda ya samu dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel