Yaki Ya Rincake: Iran Ta Harba wa Amurka Makamai Masu Linzami Sama da 10

Yaki Ya Rincake: Iran Ta Harba wa Amurka Makamai Masu Linzami Sama da 10

  • Kasashen Iran da Amurka sun kai wa juna hare-hare yayin da aka shiga rana ta biyu tun bayan dawowa da kai farmaki a tsakaninsu
  • Iran ta kai hare-hare kan sansanonin sojojin Amurka da ke Bahrain da Kuwait tare da kai hari kan wasu jiragen ruwa biyu a mashigar Hormuz
  • Rundunar IRGC ta kasar Iran ta bayyana cewa ta kai hare-haren ne domin ramuwar gayya kan sababbin hare-haren da Amurka ta kai mata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Gwamnatin Iran ta kai hari da jiragen sama marasa matuka a sansanin Sheikh Isa da ke Bahrain da sansanonin Ali Al Salem da Ahmad Al-Jaber da ke Kuwait a daren Alhamis.

Harin Iran ya biyo bayan hare-hare da Amurka ta kai kan tsibirin Qeshm da kuma tashoshin jiragen ruwa na Sirik, Jask da Bandar Abbas a Iran.

Kara karanta wannan

"Za su dandana kudarsu"; Trump ya yi sabuwar barazana ga Iran bayan musayar hare hare

Wajen da Iran ta kai hari Dubai
Hayaki na tashi a wani waje da Iran ta kai hari a Dubai a Maris 2026. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Al-Jazeera ta wallafa ceewa Tehran ta ce hare-haren Amurka sun lalata tankunan ruwa biyu tare da jikkata wata hasumiyar sadarwa.

Kasar Iran ta kai hari kan Amurka

Rundunar Iran ta IRGC ta ce ta kai hari kan jiragen saman Amurka da ke sansanin al-Azraq a Jordan da makamai masu linzami guda 12.

Iran ta ce ta kai hare-haren a daren jiya Laraba, amma rundunar sojin Jordan ta ce ta tare tare da harbo dukkan makaman masu linzamin da aka harba zuwa sansanin.

Rundunar ta ce tarkacen da suka fado daga aikin kakkabo makaman sun fadi a cikin kasar Jordan amma ba su janyo asarar rayuka ko dukiya ba.

The Guardian ta wallafa cewa tun da farko rundunar IRGC ta ce ta kai hare-hare kasashen Kuwait da Bahrain kan wasu muhimman sansanonin sojojin Amurka.

Harin Iran: Kasar Kuwait ta dauki mataki

Bayan gargadin cewa tsarin kariyar sararin samaniyarta yana dakile hare-haren abokan gaba, Kuwait ta sanar da cewa ta rufe sararin samaniyarta “na wani lokaci” sakamakon sabon rikicin da ya barke.

Kara karanta wannan

Xenophobia: Najeriya da kasashe 4 da suka fara kwaso mutanensu daga Afrika ta Kudu

Sanarwar da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Kuwait ta fitar ta ce za a karkatar da wasu jirage zuwa wasu yankuna.

Martanin Amurka bayan harin

Bayan kai farmaki Tehran, rundunar sojojin Amurka ta sanar da cewa dakarunta sun kammala sabon zagayen hare-haren da suka kai kan Iran a safiyar Alhamis.

Dakarun CENTCOM sun kai hare-hare kan tsarin sa ido na sojojin Iran, hanyoyin sadarwa da wuraren kariyar sararin samaniya a sassan Tehran.

Donald Trump tare da sojojin Amurka
Shugaba Donald Trump na yi wa sojojin Amurka jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya yi wa Iran gargadi

A wani rahoton, mun kawo muku cewa Donald Trump ya zargi Iran da jan kafa wajen tattaunawar zaman lafiya tare da yin barazanar kai mata hari mai tsanani sosai.

Ya ce za ta ga abin da zai faru a gaba, inda ya ce sun kusa cimma matsaya amma Iran ci gaba da yaudarar Amurka, tana daukar su tamkar wawaye

Tun da farko a ranar, shugaban Amurkan ya sanar da cewa Iran ta dauki lokaci mai tsawo wajen tattaunawar zaman lafiya kuma lokaci ya yi da za ta dandana kudarta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng