Latest
Wani dan bindiga ya gamu da tsautsayi yayin da ya je sace makwabcinsa, Alhaji Mohammed Makasudi a jihar Neja, mai gidan ya harbe shi a kafa yayin sace shi.
Shugaban majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele ya tabbatar da cewar majalisar dattawan za ta tantance mukaddashin gwamnan CBN, Dr. Olayemi Cardoso, a ranar Talata.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu, ya bayyana nasarar da ya samu a Kotun zaɓe da ta kowa da kowa, inda ya ce gwamnatinsa na buƙatar goyon baya.
Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya karyata jita-jitar cewa su na tattaunawa da 'yan bindiga a asirce a Zamfara kamar yadda Gwamna Dauda Lawal ya yi zargi.
Jam’iyyar PDP a jihar Lagas da dan takararta na gwamna, Olajide Adediran, sun bayyana matsayinsu dangane da nasarar Babajide Sanwo-Olu a kotun zabe.
Tsohon dan majalisar tarayya, Shehu Sani, ya soki tsige Honorable Beni Lar da sauran yan majalisar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Filato.
Wasu mutane da ke siffanta kansu da karnuka sun yi wata ganawa a kasar Jamus, sun yi ta haushi da junansu madadin magana yayin ganawar inda mutane ke ta mamaki.
Majalisar dokokin jihar Ondo ta aika wa mataimakin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa da takardar sanarwan yunkurinta na sauke shi daga kan muƙaminsa.
Alhaji Aliko Dangote ya tafka mummunar asara har Naira miliyan 525 a cikin sa'o'i 24 kacal wanda hakan ya saka shi mafi asara a Nahiyar Afirka gaba daya.
Masu zafi
Samu kari