Majalisar Dattawa Za Ta Tantance Gwamnan CBN Da Mataimakansa a Ranar Talata

Majalisar Dattawa Za Ta Tantance Gwamnan CBN Da Mataimakansa a Ranar Talata

  • Majalisar dattawan Najeriya za ta tantance sabbin shugabannin CBN da Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada a ranar Talata, 26 ga watan Satumba
  • Ofishin labaran Sanata Opeyemi Bamidele ne ya tabbatar da ci gaban a cikin wata sanarwa a ranar Litinin
  • Bamidele ya kuma ce majalisar dattawan za ta tantance sabbin ministoci biyu a ranar 3 ga watan Oktoba

FCT, Abuja - Majalisar dattawa za ta tantance tsohon shugaban kamfanin Citi Nigeria, Olayemi Cardoso, a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) a ranar Talata, 26 ga watan Satumba.

Majalisar dattawa za ta tantance gwamnan CBN
Majalisar Dattawa Za Ta Tantance Gwamnan CBN Da Mataimakansa a Ranar Talata Hoto: The Senate President - Nigeria, @Mr_JAGs
Asali: Facebook

Yan majalisar za su tantance kuma wasu mutane hudu kan kujerun mataimakan gwamnan CBN, wadanda za hadu da Cardoso wajen juya ragamar babban bankin a shekaru hudu masu zuwa, rahoton Channels TV.

Majalisar Dattawa za ta tantance dukkan wadanda aka nada bayan ta dawo hutun ta na shekara, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu Ta Bayyana Ranar Hutun Maulidi a Najeriya

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin yada labaran shugaban majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele ya fitar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A halin da ake ciki, majalisar za ta kuma tantance sabbin ministoci biyu a ranar Talata, 3 ga watan Oktoba, Sanata Bamidele ya bayyana.

Sanarwar ta ce:

"Majalisar dattawan tarayyar Najeriya za ta dawo amanta a ranar Talata, 26 ga watan Satumba, za mu duba yiwuwar tantance Dr. Cardoso a kwamitin.
"Baya ga haka, majalisar dattawan ta shirya tantance zababbun ministoci biyu - Dr. Jamila Bio Ibrahim da Mista Ayodele Olawande, a matsayin ministar matasa da karamin ministan matasa a ranar 3 ga watan Oktoba."

Cardoso Ya Fara Aiki a Matsayin Sabon Mukaddashin Gwamnan CBN

A baya mun ji cewa a hhukumance, Mista Olayemi Michael Cardoso, ya kama aiki a matsayin sabon muƙaddashin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Kara karanta wannan

Kotu Ta Raba Gardama Tsakanin Labour Party Da APC Kan Kujerar Dan Majalisa

Mista Cardoso ya hau wannan matsayin ne biyo bayan naɗin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya masa, gabanin majalisar dattawa ta tantance shi.

Jamila Bio: Abubuwa 20 a kan macen da Tinubu ya zaba ta zama ministar matasa

A wani labarin kuma, mun ji cewa da zarar an tantance Dakta Jamila Ibrahim Bio a Majalisar Dattawa, za ta zama sabuwar ministar harkokin matasa a Najeriya.

Abin da rahoton nan ya kunsa shi ne bayani kan tarihin rayuwa da siyasar Jamila Ibrahim Bio mai shirin bin tafarkin mahaifinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel