Sojan Isra'ila Ya Yi Wulakanci Mai Muni ga Yesu Almasihu, an Fara Sukar Kasar

Sojan Isra'ila Ya Yi Wulakanci Mai Muni ga Yesu Almasihu, an Fara Sukar Kasar

  • Kasar Isra'ila na cigaba da shan suka daga bangarori daban-daban bayan sojanta ya ruguza mutum-mutumin Yesu Almasihu a kasar Lebabon
  • Hakan na zuwa ne yayin da sojojin Isra'ila ke cigaba da kai farmaki sassan kasar Lebanon duk da yarjejejiyar tsagaita wuta ta kwana 10 da aka yi
  • Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da abin da jami'inta ya aikata tare da fadin matakin da za ta dauka bayan caccakar da aka mata a fadin duniya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Lebanon - Wani hoto da ya yadu sosai a kafafen sada zumunta, wanda ke nuna wani sojan Isra’ila yana ruguza mutum-mutumin Yesu Almasihu da guduma a kudancin Lebanon, ya haifar da fushin jama’a.

Mutane da dama na zargin Isra'ila da cigaba da kai hari wuraren ibada a kasar Lebanon duk da cewa an yi yarjejeniyar tsagaita wuta.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta karya yarjejeniya a Lebanon, ta kai munanan hare hare bayan jawabin Trump

Sojan Isra'ila na rusa Yesu Almasihu
Sojan Isra'ila yayin rusa mutum mutumin Yesu Almasihu a Lebanon. Hoto: @LTC_Shoshani
Source: Twitter

Martanin Isra'ila kan rusa mutum-mutumin Yesu

A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, sojojin Isra’ila sun tabbatar da sahihancin hoton da aka yada sosai a intanet, wanda ya samu sama da masu kallo miliyan biyar a dandalin X.

Bayan wani bincike na farko, an gano cewa hoton ya nuna wani soja a Kudancin Lebanon, inda Isra’ila ta kaddamar da mamaya a watan da ya gabata tare da hare-haren sama a cikin yakin hadin gwiwa da Amurka kan Iran.

Sojojin sun kara da cewa an bude bincike kan lamarin, kuma za a dauki matakan da suka dace kan wadanda abin ya shafa bisa sakamakon binciken.

An caccaki Isra'ila kan Yesu

Da yake mayar da martani kan lamarin, dan majalisar Isra’ila dan asalin Falasdinu, Ayman Odeh ya yi rubuta mai sarkakiya da ke nuna sukar lamarin.

Shi ma Ahmad Tibi da ya kasance dan majalisar Isra'ila, ya rubuta a Facebook cewa wannan ba sabon abu ba ne lura da abin da sojojin kasar suka aikata a baya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace daliban da suka je yin jarabawar JAMB

Ya ce wadanda ke rusa masallatai da majami’u a Gaza da kuma tozarta limaman Kirista a Kudus ba tare da hukunci ba, ba za su ji tsoron lalata mutum-mutumin Annabi Isa da kuma wallafa shi ba.

“Watakila wadannan masu wariyar launin fata sun koyi haka ne daga Donald Trump wajen cin mutuncin Annabi Isa da kuma sukar Fafaroma Leo?”

In ji shi.

Karin suka ga Isra'ila kan taba Yesu

Haka kuma wasu masu gwagwarmaya, malamai da marubuta sun yi Allah-wadai da wannan tozarta mutum-mutumin, wanda yake a wajen kauyen Debl da ke kudancin Lebanon, kusa da iyakar Isra’ila.

Benjamin Netanyahu a Isra'ila
Benjamin Netanyahu na yi wa 'yan Isra'ila bayani. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Al-Jazeera ta ce masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi tir da shiru da kasashen duniya suka yi kan hare-haren da sojojin Isra’ila ke kai wa wuraren ibada da alamomin addini.

An tarwatsa 'yan leke asirin Isra'ila

A wani labarin, mun kawo muku kasar Iran ta sanar da cewa tana cigaba da farautar 'yan leken asirin Isra'ila da wasu kasashen waje.

Ta sanar da tarwatsa gungun masu leken asirin da aka ce suna yi wa kasashen Isra'ila, Amurka aiki a wani samame da ta kai a wasu birane.

Iran ta yi zargin cewa 'yan leken asirin na shirin tayar da tarzoma a kasar yayin da wa'adin tsagaita wuta da ta yi da Amurka ke shirin karewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng