“Ina Mutunta Kudi”: Kyakkyawar Mata Ta Nunawa Duniya Mijinta Dan Dattijo a Bidiyo

“Ina Mutunta Kudi”: Kyakkyawar Mata Ta Nunawa Duniya Mijinta Dan Dattijo a Bidiyo

  • Wata matashiyar mata ta kasance cikin farin ciki yayin da ta dauki bidiyonta tare da mijinta dan dattijo, wanda ke cike da kamala
  • Kyakkyawar matar ta nunawa mijin nata so da kauna tsantsa yayin da take taka rawa, inda shi kuma yake zaune waje guda a bidiyon
  • Yan Najeriya da dama da suka ga bidiyon sun bayyana ra'ayoyinsu, yayin da mutane da dama suka taya ta addu'an samun farin ciki a gidan aurenta

Wata matashiya yar Najeriya wacce ta aure wani dattijo ta haddasa cece-kuce tsakanin yan Najeriya yayin da ta baje kolin mijinta.

Matashiyar, @asmawu.hamisu, ta kira dattijon da "rayuwata" sannan ta rike hannunsa a kan teburin cin abinci yayin da suke bidiyon a TikTok.

Matashiya ta nunawa duniya dattijon mijinta
“Ina Mutunta Kudi”: Kyakkyawar Budurwa Ta Nunawa Duniya Mijinta Dan Tsoho a Bidiyo Hoto: @asmawu.hamisu
Asali: TikTok

Matashiya da dattijon mijinta

Alamu sun nuna mijin yana da sanyin hali yayin da matashiyar take ta matso kyau a gaban kamara. Binciken da aka gudanar a shafinta na TikTok ya nuna tana jin dadin rayuwa tare da murza kudi yadda take so.

Kara karanta wannan

Sabon salo: Bidiyon yadda wata mata ta fito titi neman a taimake ta ta siya iPhone 15

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cikin wani bidiyon, matashiyar ta kasance sanye da doguwar riga fara irin na amare a ranar aurensu, inda shi kuma angon ya sanya farin yadi dinkin babbar riga.

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a kasa:

Ekuaamoakowaa ya ce:

"Sashin bincikena na cewa ivy ifeoma da mijinta."

Cee jay ta ce:

"Ke kadai ce...regina daniel da ivy ifeoma ne kawai za su iya ba ni shawara a duniyar nan."

Yasmin Trunesh Hussein Ndiema ta ce:

"Duk mun yarda cewa imma dai hanyar Regina Daniels ko hanyar Kanayo .O Kanayo."

HAWERO ya ce:

"Idan dai har kina cikin farin chomi."

Jordan kudus ta ce:

"Ina girmama ka kudi."

@preshchuks ta ce:

"Ke da Regina ne kawai za ku iya ba ni shawara a shekarar nan."

Chachaluv ta ce:

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Girka Abinci Iri-Iri, Ta Ce Kudinsu Miliyan 3.2 Yayin da Ta Baje Kolinsu a Bidiyo

"Ki bi kudi, soyayya za ta biyo baya na fahimce ki yar'uwa."

Matashiya Ta Girka Abinci Iri-Iri, Ta Ce Kudinsu Miliyan 3.2

A wani labari na daban, wata yar Najeriya mai girke-girke ta haddasa cece-kuce a tsakanin mutane bayan ta wallafa bidiyon abinciki da ya kai sama da naira miliyan 3.

Mai girkin (@hotmbycheft) ta sanar da cewar ranar zagayowar haihuwarta ne yayin da ta jefa abinciki a kan teburinta da taimakon hadimanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel