Muna da Kwararan Hujjojin da Zamu Tona Muku Asiri, Zamfara Ya Maida Martani Ga FG

Muna da Kwararan Hujjojin da Zamu Tona Muku Asiri, Zamfara Ya Maida Martani Ga FG

  • Gwamna Dauda Lawal ya maida zazzafan martani ga gwamnatin tarayya kan tattaunawar sulhu da 'yan bindiga a Zamfara
  • Tun da fari, gwamnan ya ce gwamnatin tarayya ta shiga tattaunawa da yan bindiga, lamarin da FG ta maida masa raddi
  • Sai dai Lawal ya ƙara fitowa ya bayyana cewa yana da ƙwararan hujjoji da zasu tabbatar da ikirarinsa na farko

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Zamfara - Gwamna Dauda Lawal, a ranar Talata, ya ce gwamnatin jihar Zamfara na da isassun hujjoji da za ta fallasa wakilan gwamnatin tarayya da suka yi tattaunawar sirri da ‘yan bindiga.

Gwamnan wanda ya yi watsi da zabin tattaunawa da ‘yan ta’adda, tun da farko ya yi kakkausar suka kan cewa Gwamnatin Tarayya ta shiga wata tattaunawa a asirce da 'yan bindiga.

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara.
Muna da Kwararan Hujjojin da Zamu Tona Muku Asiri, Zamfara Ya Maida Martani Ga FG Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Amma ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Mohammed Idris, ya zargi gwamnatin Zamfara da sanya siyasa a harkar tsaro, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Yi Magana Mai Kyau Bayan Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Da Ya Samu a Zaɓen 2023

Muna da kwararan hujjoji - Dauda Lawal

Sai dai gwamnan ya sake maida martani ga gwamnatin tarayya a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a madadinsa ranar Talata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A sanarwan, Gwamna Lawal ya ce yana da shaidun da zasu fallasa wasu jami'an gwamnatin tarayya da ke da hannu a tattaunawar sulhu da 'yan bindiga a Zamfara.

Ya kara da cewa kamata ya yi ministan yada labarai ya gudanar da cikakken bincike kafin ya caccaki gwamnatin jihar, kamar yadda Tribune ta tattaro.

Sanarwan ta ce:

"Mun nemi karin haske daga Gwamnatin Tarayya game da tattaunawar sulhu da ‘yan bindiga da wasu jami’anta suka yi ba tare da sanin gwamnatin jiha da shugabannin hukumomin tsaro ba."
“Muna da hujjoji da shaidu kan abin da ya faru tsakanin wadannan wakilan FG da ‘yan bindiga a lokacin da suka tattauna a wurare da dama a fadin jihar Zamfara."

Kara karanta wannan

Badaru Ya Yi Zaffafan Martani Ga Gwamnan PDP Kan Sace Dalibai A Zamfara, Ya Fadi Matakin Gaba

“Abin takaici ne yadda ministan yada labaran ya karyata ikirarin mu ba tare da tantance shi ba tukuna. Abin da ya dace ya yi a matsayinsa na kwararre shi ne ya hada kai da hukumomin da abin ya shafa don tabbatar da sahihancin zancen."
“Muna so mu fayyace cewa wadanda ke jagorantar tattaunawar sirri da ‘yan bindiga a Zamfara su ke siyasantar da matsalar tsaro ba gwamnatin jihar ba."

Gwamna Lawal ya ƙara da cewa zaman sulhu da 'yan bindiga babban kuskure ne da gwamnati ba zata lamurci aikata shi ba, kana ya yi kira ga FG ta ɗauki mataki mai tsauri.

Lagos: Gwamna Sanwo-Olu Ya Yi Maraba da Hukuncin Kotun Zabe

A wani rahoton Gwamnan jihar Legas ya maida martani jim kaɗan bayan Kotun zabe ta tabbatar da nasarar da ya samu a zaben watan Maris.

Babajide Sanwo-Olu, ya yaba da hukuncin Kotun inda ya ayyana shi da nasara ga kowane ɗan jihar Legas.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Faɗi Wasu Ƙusoshin Gwamnatin Tinubu Da Suka Fara Tattaunawa Da 'Yan Bindiga

Asali: Legit.ng

Online view pixel