Yadda Ta Leko Ta Koma da Iran Ta Yi kan Mashigar Hormuz Ta Rikita Lissafi a Najeriya
- An yi hasashen samun raguwar farashin man fetur a Najeriya bayan Iran ta bude mashigar ruwa ta Hormuz
- Kakakin kungiyar masu gidajen mai ta Najeriya ya nuna cewa farashin man fetur na iya dawowa kasa da N1000
- Sai dai, wannan hasashe bai tabbata ba bayan da Iran ta yanke shawarar sake rufe mashigar ruwan ta Hormuz
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shawarar da Iran ta yanke na sake rufe mashigar ruwa ta Hormuz ta dakile fatan da ake da shi na cewa farashin man fetur zai fadi a Najeriya.
An bude mashigar ta Hormuz ne a ranar Jumma’a biyo bayan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka.

Source: Getty Images
An yi hasashen raguwar farashin fetur
Jaridar The Punch ta ce dillalan man fetur sun yi hasashen a baya cewa farashin fetur zai iya raguwa daga N1,250 zuwa kusan N900 lokacin da aka bude mashigar a ranar Juma’a, 17 ga watan Afirilun 2026.
Kakakin kungiyar masu gidajen mai na Najeriya, Joseph Obele, ya bayyana a ranar Juma’a cewa farashin danyen mai ya ruguje biyo bayan sake bude mashigar.
Obele ya tuna cewa farashin fetur yana kusan N800 kafin 28 ga watan Fabrairu, lokacin da rikicin ya fara, inda ya nuna kyakkyawan fatan cewa za a samu gagarumin ragi idan har lamarin ya dore.
“Tare da sake bude mashigar Hormuz, ya kamata ‘yan Najeriya su yi tsammanin raguwa mai ma’ana a farashin fetur. Fetur zai fadi kasa da N1,000 nan da mako mai zuwa, watakila ma zuwa N900 a kowace lita."
"Kada ku manta cewa man yana N800 da doriya kafin rikicin Gabas ta Tsakiya. Yanzu da yakin ya kare, ya kamata mu yi tsammanin komawa ga wannan tsarin farashin."
- Joseph Obele
Sake rufe mashigar Hormuz ya rikita lissafi
Amma a ranar Lahadi, 19 ga watan Afirilun 2026, Obele ya bayyana cewa sake rufe mashigar Hormuz ya ruguza fatan da ake da shi na hasashen faduwar farashin.
Obele ya ce a halin da ake ciki yanzu, farashin zai ci gaba da zama yadda yake, har sai lokacin da Iran da Amurka suka amince kan tsagaita wuta mai dorewa.

Source: Getty Images
Duk da haka, cewa ba a samu wani gagarumin tashin farashin mai ba tun ranar Asabar lokacin da Iran ta sake rufe mashigar.
A cewar shafin oilprice.com, an sayar da danyen mai na Brent akan $90 kowace ganga ranar Lahadi, wanda ya tashi daga $88 kafin sake rufe mashigar ta Hormuz.
Idan ba a manta ba dai farashin Brent ya kai $95 har zuwa safiyar ranar Juma’a.
Matatar Dangote ta rage farashin fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar Dangote da ke Legas ta sanar da janye karin farashin man fetur da ta yi.
Matatar man Dangote ta janye karin da ta yi, inda ta maida farashin kowace litar zuwa zuwa ₦1,200.
Matakin janye karin ya biyo bayan gagarumar faɗuwar farashin ɗanyen mai da aka samu a kasuwar duniya sakamakon tsagaita wutar Iran da Amurka a yakin Gabas ta Tsakiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

