Daga Karshe Trump Ya Fadi Dalilin da Ya Sanya Ya Fara Yaki da Iran
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi tsokaci kan batun cewa Isra'ila ce ta sanya shi ya fara yaki da Iran
- Donald Trump ya bayyana cewa ko kadan Isra'ila ba ta lallaba shi ba domin ya fara kai hare-hare kan kasar Iran
- Shugaban na Amurka ya fito ya kuma soki kafafen yada labaran kasar masu sukar yakin da ake yi da Iran a Gabas ta Tsakiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban Amurka Donald Trump ya yi magana kan batun cewa Isra'ila ce ta sanya shi ya fara yaki da Iran.
Trump ya musanta cewa Isra'ila ce ta ja shi cikin yaƙi da Iran, yayin da yake fuskantar ƙaruwar suka kan rikicin, har ma daga ɓangarorin magoya bayansa.

Source: Getty Images
Shugaba Trump ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Litinin, 20 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Iran ta sake kunyata Trump a idon duniya ana shirin sake zaman sulhu
Meyasa Trump ya yaki Iran?
Trump ya bayyana cewa ko kadan Isra'ila ba ta lallaba shi domin sanya shi fara yaki da kasar Iran.
"Isra'ila ba ta taɓa lallashi na in shiga yaƙi da Iran ba, sakamakon abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoba ne, wanda ya ƙara ƙarfafa tsohon ra'ayina na cewa Iran ba za ta taba samun makamin nukiliya na, shi ya ja ni."
"Ina kallo da karanta sharhin masana labaran karya da sakamakon binciken jin ra'ayin jama'a cikin rashin yarda."
"Kaso 90 na abin da suke faɗa ƙarya ne da tatsuniyoyi, kuma an tafka maguɗi a binciken ra'ayin, kamar yadda aka tafka maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa na 2020."
"Kamar dai sakamakon da aka samu a Venezuela, wanda kafafan yaɗa labarai ba sa son magana a kai, sakamakon da za a samu a Iran zai kasance abin mamaki, kuma idan sababbin shugabannin Iran (Canjin Gwamnati!) suna da wayo, Iran za ta iya samun babbar makoma mai albarka! Shugaba DJT."
- Shugaba Donald Trump
Trump na shan suka kan yaki da Iran
Babu wata shaida a bainar jama'a da ta haɗa Iran kai-tsaye da hare-haren Hamas na 7 ga Oktoba, 2023, a kan Isra'ila.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta ce ita kanta babbar jami'in leken asiri ta gwamnatin Trump, Tulsi Gabbard, ta ba da shaida a gaban Majalisa a watan Maris cewa Iran ba ta kera makamin nukiliya.
A cikin watanni takwas kafin yaƙin Iran, Trump ya riƙa faɗa akai-akai cewa hare-haren saman da Amurka ta kai wa ƙasar a watan Yuni sun "ruguza" shirinta na nukiliya.
Da yawa daga cikin masu sukar Trump sun bayyana cewa Iran ba ta kasance barazana ta kusa ga Amurka ba, kuma yaƙin kawai yana ciyar da muradun Isra'ila gaba ne a madadin tsaro da ci gaban Amurkawa
Matsayar Iran kan sake tattaunawa da Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nuna shakku kan shiga zagaye na biyu na tattaunawa da Amurka.
Iran ta tuna yadda Amurka ta kai mata hare-hare a daidai lokacin da ake tsaka da tattaunawar diflomasiyya, tana mai cewa ba za ta taba manta wa da hakan ba.
Hakazalika, Iran ta zargi Amurka da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma rashin nuna gaskiya a harkokin diflomasiyya.
Asali: Legit.ng

