Jam'iyyar ADC Ta Yi Maganar Hadewa da PRP, Ta Bayyana Shirin da Take Yi

Jam'iyyar ADC Ta Yi Maganar Hadewa da PRP, Ta Bayyana Shirin da Take Yi

  • An yada wasu bayanai masu nuna cewa jam'iyyar ADC mai adawa na shirin hadewa da takwararta ta PRP
  • Sakataren yada labarai na ADC, Bolaji Abdullahi, ya fito ya yi karin haske kan batun hadewa da jam'iyyar PRP
  • Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa ADC ta mayar da hankali wajen ganin an soke matakin da hukumar INEC ta dauki kan shugabancin jam'iyyar

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta yi martani kan batun cewa tana shirin hadewa da takwararta ta PRP gabanin zaben 2027.

Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta bayyana cewa ba ta tunanin kulla wani ƙawance da takwararta ta PRP.

ADC ta musanta batun hadewa da PRP
Rauf Aregbesola, David Mark da Atiku Abubakar a wajen taron jam'iyyar ADC Hoto: Hon Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a wani rubutu da sakataren yada labarai na kasa na ADC, Bolaji Abdullahi, ya yi a shafinsa na X a ranar Litinin, 20 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Masoya Kwankwaso da Obi sun yi riga malam masallaci, sun fara shirin kamfen

Ana rade-rade kan ADC

Tun daga ranar 1 ga Afrilu, lokacin da INEC ta soke amincewa da shugabancin ADC ƙarƙashin David Mark ake ta rade-radi kan makomar jam'iyyar.

An yi ta samun rade-radin cewa shugabannin adawa na iya neman haɗewa da wasu jam’iyyun siyasa, ciki har da PRP, gabanin babban zaɓen 2027.

Me ADC ta ce kan hadewa da PRP?

Bolaji Abdullahi ya bayyana iƙirarin a matsayin ƙarya, inda ya nuna cewa shugabancin haɗakar jam’iyyun ba sa cikin wata tattaunawa da wata jam’iyyar siyasa a halin yanzu.

“Hankalinmu ya karkata ga wani labari da ke yawo cewa jam’iyyar ADC tana tattaunawa da wata jam’iyyar siyasa, musamman PRP sakamakon jiran hukuncin kotu. Muna so mu bayyana karara cewa wannan ba gaskiya ba ne."

- Bolaji Abdullahi

Wane aiki ADC ta tasa a gaba?

Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa haɗakar jam’iyyun tana ci gaba da mayar da hankali ne wajen ƙalubalantar abin da ya kira “matakin sabawa doka” da INEC da wasu da ake zargi wakilan jam’iyya mai mulki ne suka ɗauka a kan shugabancinta.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya yi zarge zarge kan Kwankwaso, ya fadi yadda ya ci amanar Arewa

“Shugabancin haɗakar ba ya gudanar da kowace irin tattaunawa da kowace jam’iyyar siyasa a halin yanzu. Muna da cikakken kudurin tabbatar da cewa matakin sabawa doka da INEC da sauran wakilan jam’iyya mai mulki suka ɗauka a kan shugabancinmu an soke shi."

- Bolaji Abdullahi

Kakakin na ADC ya bayyana cewa jam’iyyar ta yi amanna cewa soke wannan mataki yana da matuƙar muhimmanci wajen kiyaye bin doka da oda da kuma kare tsarin dimokuraɗiyya na jam’iyyu da dama a Najeriya.

ADC na son soke matakin INEC a kanta
Sakataren yada labarai na ADC na kasa, Bolaji Abdullahi Hoto: @BolajiADC
Source: Twitter

ADC za ta fadada hadaka

Yayin da yake nanata shirye-shiryensu na faɗaɗa haɗakar domin karɓar wasu ɓangarorin adawa, Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa ADC ba ta tunanin barin dandalinta.

“Duk wata shawara da ke nuna cewa muna tunanin barin ADC magana ce ta hasashe, kuma ya kamata a yi watsi da ita."

- Bolaji Abdullahi

Jam’iyyar ta kuma nuna kwarin gwiwa ga ɓangaren shari’a, inda ta yi kira gare su da su jure duk wani matsin lamba kuma su tsaya tsayin daka wajen kare dimokuraɗiyya.

ADC ta yi wa Tinubu martani

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta yi zazzafan martani ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Gabanin 2027, ADC ta fada wa Tinubu maganar da za ta jefa masa tsoron 'yan adawa

ADC ta bayyana cewa kalaman shugaban suna nuna tsantsar fargaba da damuwa ne maimakon kwarin gwiwar da yake nuna wa a fili.

A cewar ADC, akwai dalilai da dama da ya kamata su jefa shugaban ƙasa a cikin tsoro kafin babban zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng