Majalisar Dokokin Ondo Aike da Mataimakin Gwamna da Sakon Shirin Tsige Shi

Majalisar Dokokin Ondo Aike da Mataimakin Gwamna da Sakon Shirin Tsige Shi

  • Majalisar dokoki ta aike a takardar sanarwa ga mataimakin gwamnan jihar Ondo kan yunƙurin tsige shi daga kan muƙaminsa
  • Wannan na zuwa ne awanni kaɗan bayan Mista Lucky Aiyedatiwa, ya roƙi Kotu ta dakatar da shirin da majalisa ke yi a kansa
  • A takardar sanarwan, majalisar ta gaya wa mataimakin gwamnan zarge-zargen da take masa ciki harda rashin ladabi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ondo - Daga karshe majalisar dokokin jihar Ondo ta mika wa mataimakin gwamnan jihar, Mista Lucky Aiyedatiwa, sanarwar tana shirin tsige shi.

Mataimakin gwamnan ya karbi sanarwar ne a ranar Litinin, ta hannun mai magana da yawun majalisar, Olatunji Oshati, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Majalisa ta tabbatar da shirin tsige mataimakin gwamna a hukumance.
Majalisar Dokokin Ondo Aike da Mataimakin Gwamna da Sakon Shirin Tsige Shi Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

Sanarwan yunƙurin tsige Aiyedatiwa daga matsayin mataimakin gwamnan jihar Ondo na ɗauke da sa hannun mambobi 11 daga cikin 26 na majalisar dokokin.

Kara karanta wannan

Yan Majalisa Sun Karbi Cin Hanci Domin Tsige Mataimakin Gwamnan APC? Gaskiya Ta Bayyana

Jam’iyya mai mulki a jihar Ondo watau APC ce ke da rinjaye a majalisar da kujeru 22 yayin da jam'iyyar PDP ke da kujeru hudu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Meyasa majalisar ke tunƙurin tsige mataimakin gwamnan?

A cewar takardar sanarwan mai ɗauke da sa hannun shugaban majalisar, Oladiji Adesanmi, tuhume-tuhumen da ake wa mataimakin gwamnan sun ƙunshi rashin ɗa'a da koƙarin ruguza gwamnatin Ondo.

Sauran zarge-zargen da majalisar ta rataya masa sun haɗa da wadaƙa da kuɗaɗe da kuma buga labarin a kafafen watsa labarai, wanda ya haifar da tababa kan nagartar gwamna Rotimi Akeredolu.

Sanarwan ta ce:

"Bisa tanadin sashi na 188(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya 1999 da aka yi wa kwaskwarima, ya kamata a miƙa wa mataimakin gwamna kwafin wannan takarda domin ya kare kansa kan zarge-zargen."

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Hukumar DSS Ta Kama Ɗan Majalisar PDP Bisa Zargin Hannu a Kashe Rayuka Sama da 20

A halin da ake ciki, mataimakin gwamnan ya kai karar majalisar gaban Kotu dangane da shirin tsige shi, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Mista Aiyedatiwa, a karar da lauyansa, Ebun-Olu Adegboruwa, (SAN) ya shigar a babbar kotun Akure, ya bukaci kotu ta bada umarnin hana majalisa ta sauke shi daga kujerarsa.

Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Sahihancin Nasarar Gwamnan APC a Zaben 2023

A wani rahoton kuma Kotun sauraron ƙarar zaben gwamna ta yanke hukunci kan nasarar gwamna Sanwo-Olu na jihar Legas.

Kwamitin alkalai uku karkashin mai shari'a Arum Ashom ta kori kararrain yan takarar LP da PDP, ta tabbatar da nasarar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel