Dangote Ya Tafka Asarar Naira Biliyan 525 A Cikin Sa'o'i 24 Saboda Sabbin Tsare-tsare

Dangote Ya Tafka Asarar Naira Biliyan 525 A Cikin Sa'o'i 24 Saboda Sabbin Tsare-tsare

  • Dangote ya tafka asarar Naira biliyan 525 a cikin sa'o'i 24 wanda hakan ya saka shi a matsayin farko a tafka asara
  • Sauran attajiran kasar Najeriya da su ka hada da Abdussamad Rabiu da Mike Adenuga su ma sun tafka asara
  • Sai kuma Johan Rupert da Nicky Oppenheimer na kasar Afirka ta Kudu da kuma 'yan uwan juna Naguin da Nassef

FCT, Abuja - Gwamnatin Najeriya ta dauki wasu matakai da su ka kawo cikas ga kasuwancin attajiran kasar.

Kafin daukar wannan mataki, mafi yawan attajiran na cikin jerin masu kudi 500 a duniya, wanda Dangote ke jagorantarsu a Najeriya da kusan Dala biliyan 21, Legit ta tattaro.

Dangote ya tafka asarar Naira miliyan 525
Dangote Ya Tafka Asarar Naira Biliyan 525 A Cikin Sa'o'i 24. Hoto: Anadolu Agency.
Asali: Getty Images

Asarar nawa Dangote ya yi a sa'o'i 24

Abokin hamayyarsa, Abdussamad Rabiu mai kamfanin BUA ya na mataki na biyu da makudan kudade har Naira biliyan 5.

Kara karanta wannan

Gaskiya Kenan: ASUU Ta Yi Kakkausar Martani Kan Karin Kudin Jami'o'i, Ta Fadi Abin Da Zai Faru

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da Mike Adenuga ke mataki na uku wanda shi ne na bakwai a jerin masu kudi a Nahiyar Afirka.

Dangote da Rabi'u da kuma Adenuga ba su kadai ne su ka yi asara ba a Nahiyar Afirka saboda tsare-tsaren tattalin arziki.

Asarar sauran attajiran idan aka kwatanta da Dangote?

Rahoton Bloomberg ya tattaro cewa Johan Rupert ya tafka asarar Dala miliyan 10 a cikin kwanaki 10 kacal saboda wasu tsare-tsare a kasar.

Rahoton ya kuma tabbatar da cewa dan Afirka ta Kudu, Nicky Oppenheimer ya yi asarar Dala miliyan 150 shi ma a cikin kankanin lokaci.

Sauran sun hada da dan kasar Masar, Naguib Sawiris da asarar Dala miliyan 99 sai Nassef Sawiris da asarar Dala dubu 8.4 sai Natie Kirsh da asarar Dala dubu 95.

Dangote ya tafka asarar Naira biliyan 483 a cikin sa'o'i 24

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Samo Sabon Bashi Na Dala Miliyan 700 Daga Bankin Duniya, Cikakken Bayani

A wani labarin, Mamallakin kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya tafka asarar Dala miliyan 613 a cikin sa'oi 24 kacal saboda sauyin tattalin arziki a kasar.

Kudaden idan aka kwatanta da kudin Najeriya ya kai Naira biliyan 483 kenan cikin ko wane minti daya da ta shude.

Mujallar Forbes ce ta wallafa hakan inda ta ce yanzu Dangote ya na da makudan kudade har Dala biliyan 10.5 kenan a duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel