"Najeriya Ta Yi Rashi," Tinubu Ya Yi Magana Mai Ratsa Zuciya da Galadima Ya Mutu
- Najeriya ta rasa babban jigo a fannin harkokin wasanni, Alhaji Ibrahim Galadima, wanda ya rasu a garin Kano ranar Asabar yana da shekaru 78
- Shugaba Bola Tinubu ya nuna alhininsa game da rasuwar Galadima, wanda ya taba rike mukamin shugaban NFF da kuma kwamishina a Kano
- Tinubu ya ce za a ci gaba da tunawa da kyawawan ayyukan Galadima a matsayin babban mai kishin ƙwallon ƙafa da kuma jagora abin koyi ga matasa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano – Duniyar wasanni a Najeriya ta tsinci kanta a cikin yanayi na alhini da jimami biyo bayan rasuwar tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa (NFA), Alhaji Ibrahim Galadima.
Galadima ya riga mu gidan gaskiya ne a ranar Asabar a birnin Kano yana ɗan shekara 78, bayan shafe shekaru da dama yana bayar da gudunmawa ga ci gaban wasanni.

Source: Getty Images
Tsohon shugaban NFF ya rasu
Tsohon sakataren hukumar NFF, Sani Toro, ne ya fara tabbatar da labarin rasuwar babban mai gudanar da wasannin, in ji rahoton The Nation.
Toro ya bayyana Galadima a matsayin mutum mai daraja wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen ɗaukaka martabar ƙwallon ƙafar Najeriya, inda ya yi addu'ar Allah ya jiƙansa da gafararsa.
Ibrahim Galadima ya riƙe muƙamai daban-daban a matakin jiha da na tarayya, kamar yadda rahotanni suka nuna.
Ya taɓa zama shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano sannan ya riƙe muƙamin kwamishina har sau biyu a jihar.
Daga shekarar 2002 zuwa 2006, ya jagoranci hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa (wadda yanzu ta koma NFF) a matsayin shugaba, inda aka samu nasarori daban-daban a lokacin sa.
Bayan ya yi ritaya daga aikin gwamnati, Galadima ya ci gaba da amfanar da al'ummarsa, inda aka naɗa shi sarautar Galadiman Fagge, da ke jihar Kano.

Kara karanta wannan
An yi babban rashi a jihar Kano, tsohon shugaban NFF ta Najeriya ya riga mu gidan gaskiya
Tinubu ya girgiza da mutuwar Galadima
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana baƙin cikinsa game da rasuwar babban jigo a fannin wasanni kuma jagoran al'umma, Alhaji Ibrahim Galadima.
A cikin sanarwar da mai tallafawa shugaban kasar kan kafofin sada zumunta, Abdulaziz Abdulaziz ya fitar a shafinsa na Facebook, Tinubu ya bayyana rasuwar marigayin, wanda ɗan asalin jihar Kano ne, a matsayin babban rashi ga harkar wasanni da kuma Najeriya baki ɗaya.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa gudunmawar da Galadima ya bayar wajen haɓaka ƙwallon ƙafar Najeriya, tun daga matakin farko har zuwa matakin ƙwararru, za ta ci gaba da rayuwa a zukatan ƴan ƙasa na tsawon lokaci.

Source: Twitter
Saƙon ta'aziyyar Tinubu ga jihar Kano
A cikin saƙon nasa, Shugaba Tinubu ya miƙa ta'aziyya ga iyalan marigayin, da gwamnati, da kuma daukacin al'ummar jihar Kano.
Shugaban ya kuma haɗa da daukacin mabiya harkar wasanni a cikin Najeriya da ma wajenta, waɗanda wannan rashi ya shafa kai-tsaye.

Kara karanta wannan
Saraki ya jefi gwamnatin Buhari da zargi kan fashin Offa, ya fallasa gwamnan Kwara
Shugaban ya yi addu'ar Allah ya ba wa iyalan marigayin haƙurin jure wannan rashi, sannan ya bayyana cewa za a ci gaba da tunawa da kyawawan ayyukan Galadima a matsayin babban mai kishin ƙwallon ƙafa.
Tuna baya: Mukamin da Ganduje ya ba Galadima
Idan ba a manta ba, a shekarar 2019, Legit Hausa ta ruwaito cewa, gwamna Kano Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadi da sake nadin wasu shugabannin hukumomin gwamnati a jihar.
Daga cikin wadanda aka nada akwai Alhaji Ibrahim Galadima, wanda aka ba mukamin shugaban hukumar wasanni na jihar Kano.
Babban sakataren yada labaran gwamnan a wancan lokaci, Malam Abba Anwar ne ya sanar da hakan a sanarwar da ya fitar ranar 16 ga watan Yuli, 2029 a Kano.
Asali: Legit.ng
