Badaru Ya Karyata Jita-jitar Cewa Su Na Tattaunawa Da 'Yan Bindiga A Asirce

Badaru Ya Karyata Jita-jitar Cewa Su Na Tattaunawa Da 'Yan Bindiga A Asirce

  • Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya karyata zargin Gwamnatin Tarayya na tattaunawa da 'yan bindiga a sirrance
  • Wannan na zuwa ne bayan sace-sace da kisan mutane na kara kamari a jihar musamman sace dalibai da aka yi a kwanan nan
  • Da ya ke martani, ministan tsaro, Badaru Abubakar ya musanta zargin inda ya ce sun himmatu wurin kwato daliban cikin gaggawa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya musanta zargin tattaunawa da 'yan bindiga a sirrance.

Badaru ya bayyana haka ne yayin martani ga Gwamna Dauda Lawal kan zargin tattaunawa da 'yan bindigan ba tare da sanin gwamnatin jihar ba.

Badaru ya yi martani kan zargin tattaunawa da 'yan bindiga a Zamfara
Badaru Ya Yi Martani Kan Jita-jitar Tattaunawa Da 'Yan Bindiga. Hoto: Badaru Abubakar, Bello Matawalle.
Asali: Twitter

Meye Badaru ya ce game da 'yan bindiga a Zamfara?

Ya yi watsi da jita-jitar inda ya ce Gwamnatin Tarayya ta himmatu wurin dakile matsalar tsaro a kasar, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Abin Ya Girma: Tsohuwar Ministar Buhari Ta Shiga Gangamin Ceto Daliban Jami'ar Da Aka Sace A Zamfara

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daraktan hulda da jama'a na ma'aikatar tsaro, Attari Hope shi ya bayyana haka a jiya Litinin 25 ga watan Satumba.

Ya ce Gwamnatin Tarayya ta na aiki ba dare ba rana don tabbatar da ceto daliban da aka sace a jihar Zamfara.

Badaru ya ce:

"Wannan jita-jita karyace kuma ba ta da makama, ma'aikatar tsaro ba ta wakilta kowa ba don tattaunawa da 'yan bindiga a madadin gwamnati."

Meye martanin Matawalle kan 'yan bindiga a Zamfara?

Ya kara da cewa Shugaba Tinubu ya ba da umarni ga jami'an tsaro da su kwato daliban da aka kama a jihar Zamfara.

Ya ce umarnin Shugaba Tinubu ya sa an yi nasarar kwato daliban guda 13 wanda hakan ya faru ne saboda kwarewar rundunar sojoji.

Ministan ya kuma jajantawa iyalan wadanda abin ya rutsa da su inda ya ba su hakuri kan wannan jarrabawa, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Faɗi Wasu Ƙusoshin Gwamnatin Tinubu Da Suka Fara Tattaunawa Da 'Yan Bindiga

A bangarenshi, karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi Allah wadai da sace daliban da aka yi inda ya bukaci jami'an tsaro su yi gaggawar kwato su.

Dauda Lawal ya zargin FG da tattaunawa da 'yan bindiga

A wani labarin, Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya zargi cewa wasu kusoshin gwamnati na tattaunawa da 'yan bindiga ba tare da sanin shi ba.

Gwamnan ya yi wannan zargin ne yayin da rashin tsaro ke kara ta'azzara a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel