Edo: Tsohon Ministan Ayyuka, Onolememen, Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP

Edo: Tsohon Ministan Ayyuka, Onolememen, Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP

  • Babbar jam'iyyar adawa PDP ta ƙara shiga tasku yayin da tsohon Ministan ayyuka ya sanar da ficewa daga jam'iyyar a hukumance
  • Chief Mike Oziegbe Onolememen ya tura wasiƙar fita daga PDP ga shugaban jam'iyya na ƙasa da na jiharsa ranar 25 ga watan Satumba
  • Ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bayan dogon nazari kan rikicin cikin gida da ke faruwa a PDP

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Edo - Tsohon Ministan ayyuka a Najeriya kuma babban jigon jam'iyyar PDP, Chief Mike Oziegbe Onolememen, ya yi murabus daga kasancewarsa mamban jam'iyyar.

Onolememen ya tabbatar da fice wa daga jam'iyyar PDP a wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 25 ga watan Satumba, 2023, kamar yadda jaridar Leadership ta tattaro.

Tsohon Ministan ayyuka a Najeriya, Mike Oziegbe, ya bar PDP.
Edo: Tsohon Ministan Ayyuka, Onolememen, Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP Hoto: leadership
Asali: UGC

Meyasa ya yanke shawarin fita daga PDP?

Tsohon ministan ya bayyana cewa ya yanke shawarin barin jam'iyyar PDP ne saboda yawan rigingimun cikin gida da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Mai Zafi Kan Gobarar Kotun Koli, Ta Bayyana Abinda Take Zargi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya tura wasiƙar fita daga PDP zuwa ga shugaban jam'iyya reshen jihar Edo, Dakta Tony Aziegbemi, haka nan kuma ya tura kwafin takardar zuwa ga shugaban PDP na ƙaramar hukumarsa.

Bugu da ƙari, tsohon Ministan ya sake tura takardar ga shugaban PDP na mazaɓar Sanatan da ya fito da kuma muƙaddashin shugaban jam'iyya na ƙasa, Umar Damagun.

Wace jam'iyya zai koma bayan barin PDP?

Onolememen na ɗaya daga cikin ƙusoshin da suka kafa jam’iyyar PDP tun 1998, amma bai bayyana jam’iyyar da zai shiga ba a halin yanzu, PM News ta rahoto.

Wani sashin wasiƙar ya ce:

"Bayan na yi nazari sosai kan rigingimun da ke faruwa a jam’iyyar tare da tuntubar masu ruwa da tsaki daga mazabata, abokan siyasa, abokai, da ‘yan uwa, na yanke shawara ta ƙarshe."

Kara karanta wannan

Dakatar Da Kwankwaso: Jigon NNPP Ya Magantu, Ya Bayyana Abin Da Jam'iyyar Ke Bukata

"Ina so na yi amfani da wannan damar na miƙa godiya ta ga duk wanda ke cikin tafiyar siyasa ta tun lokacin da na shiga Jam'iyyar PDP a 1998."

"Muna Zargin Akwai Wata Manaƙisa a Gobarar Kotun Koli" PDP Ta Maida Martani

A wani rahoton kuma kun ji cewa Jam'iyyar PDP ta maida martani kan ibtila'in gobara da ya ƙone wani sashi a Kotun ƙolin Najeriya.

Kakakin PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce suna zargin akwai lauje cikin naɗi duba da manyan kararrakin da ke gaban Kotun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel