Mata 15 Sun Zama Dorebobin Manyan Motoci a Kamfanin Ashaka
Gombe - Kamfanin Lafarge Africa Plc ya yaye mata 15 da suka kammala horon tukin manyan motoci a karkashin shirin Women on Wheels a jihar Gombe.
An gudanar da bikin yaye direbobin ne a ranar 9 ga Afrilu, 2026 a kamfanin Ashaka Cement da ke Jihar Gombe.
Shirin na da nufin ƙarfafa mata da kuma magance ƙarancin direbobin manyan motoci a Najeriya
Hoton da aka ba mata direbobin 15
Matan da suka zama direbobin sun samu horo mai zurfi kan dabarun tukin manyan motoci da kiyaye dokokin tsaron hanya, tare da bin ƙa’idojin aiki na zamani.
Shirin ba kawai yana rage gibin direbobi ba ne, har ma yana inganta tsaron hanya da ƙarfafa shigar mata a harkar sufuri da gine-gine.
Gwamnatin Gombe ta yaba da shirin
Mataimakin gwamnan Jihar Gombe, Mannasseh Jatau, ya yaba da ƙoƙarin kamfanin Lafarge wajen ba mata dama da ƙarfafa al’umma.
Ya ce shirin ya nuna yadda za a magance matsalolin zamantakewa ta hanyar samar da dama ga mata masu tasowa.

Kara karanta wannan
"Wasun su hotiho ne": Tsohon dan majalisa ya gargadi Tinubu kan dogaro da gwamnoni a 2027
Shugaban kamfanin Lafarge Africa, Lolu Alade-Akinyemi, ya ce wannan nasara wata alama ce ta ci gaba da sauyin da ake samu a fannin sufuri da gine-gine.
Ya bukaci wadannan matan 15 da su ci gaba da aiki da ƙwazo, yana mai cewa sun karya tsofaffin al’adu da ke hana mata shiga irin wannan sana’a.
Darakta na sashen sufuri na kamfanin, Osazemen Aghatise, ya ce shirin ya buɗe sabuwar dama ga mata, yana nuna cewa ƙwarewa ba ta da alaƙa da jinsi.
Fiye da mata 100 sun zama direbobi
Ya ƙara da cewa yanzu akwai fiye da mata 100 da ke aiki a matsayin direbobi a kamfanin.
Manajan kamfanin Ashaka Cement, Ibrahim Aminu, ya bayyana wannan a matsayin babban ci gaba ga yankin Arewa maso Gabas
Ya ce shigar da matan cikin aikin tukin manyan motoci zai taimaka wajen inganta harkar sufuri da rage ƙarancin direbobi.
Jagorar daliban da suka kammala hoton tukin, Judith Baka, ta gode wa kamfanin Lafarge bisa damar da aka ba su, tare da yaba wa malamai da masu horaswa
Manyan bakin da suka halarci taron yaye direbobi matan sun haɗa da Sarkin Funakaye, Yakubu Kwairanga, da jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.
Tun bayan ƙaddamar da shirin a 2019, kamfanin Lafarge ya horar da mata sama da 100 a fannin tukin manyan motoci, yana ci gaba da ƙarfafa mata da inganta harkar gine-gine a Najeriya.
Asali: Legit.ng