Lagos: Gwamna Sanwo-Olu Ya Yi Maraba da Hukuncin Kotun Zabe

Lagos: Gwamna Sanwo-Olu Ya Yi Maraba da Hukuncin Kotun Zabe

  • Gwamnan jihar Legas ya maida martani jim kaɗan bayan Kotun zabe ta tabbatar da nasarar da ya samu a zaben watan Maris
  • Babajide Sanwo-Olu, ya yaba da hukuncin Kotun inda ya ayyana shi da nasara ga kowane ɗan jihar Legas
  • Ya kuma yi kira ga sauran 'yan takara su haɗa kai da gwamnatinsa domin gina jihar da su ke fata

Jihar Legas - Murna ta mamaye jam'iyyar APC reshen jihar Legas biyo bayan hukuncin da Kotun sauraron kararrakin zaben gwamna ta yanke ranar Litinin.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Babajide Sanwo-Olu da mataimakinsa, Obafemi Hamzat, a zaɓen ranar 18 ga watan Maris, 2023, The Nation ta rahoto.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.
Lagos: Gwamna Sanwo-Olu Ya Yi Maraba da Hukuncin Kotun Zabe Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Asali: Twitter

Ɗan takarar gwamna a inuwar PDP, Olajide Adediran, da takwaransa na jam'iyyar LP, Gbadebo Rhodes-Vivour, su ne suka ƙalubalanci sakamakon da INEC ta bayyana.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Benue Ya Fusata Kan Sace Manyan Yan Siyasa a Jiharsa, Ya Ba Jami'an Tsaro Muhimmin Umarni

Gwamna Sanwo-Olu ya yaba da hukuncin Kotu

Gwamnan ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ta kowa da kowa, inda ya bukaci ‘yan Legas da su ba gwamnatinsa hadin kai domin kawo ci gaba a jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanwo-Olu, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a gidan gwamnati da ke Ikeja bayan yanke hukuncin, ya yaba wa alkalan da suka karanto cikakken hukunci.

A rahoton Premium Times, Gwamnan ya ce:

"Ya ɗauki dogon lokaci mai tsauri amma muna godiya da aka saurari muryar mutanen jihar Legas kuma aka tabbatar da muradinsu. Ni da Mataimakin Gwamna muna da gata sosai kuma muna godiya ga ’yan Legas."
"Wannan nasara ce ta kowa da kowa, babu wanda ya yi nasara ko ya faɗi, dama ce ta hidima. Kuma za mu ci gaba da yin aiki tukuru don isar da romon dimokuradiyya ga jama’a.”

Kara karanta wannan

Shugabanni da Kusoshin Jam'iyya Sun Jingine Tsohon Gwamna, Sun Koma Inuwar APC

"Har ila yau, muna miƙa hannu ga 'yan uwanmu 'yan takara, su jingine komai su haɗa hannu damu wajen gina jihar Legas da muke fata."

Dangote Ya Yi Magana Kan Batun Karya Farashin Buhun Siminti a Najeriya

A wani rahoton na daban Kamfanin Ɗangote ya bayyana gaskiya kan rahoton da ke yawo cewa ya karya farashin buhun siminti daga N5,000 zuwa N2,500.

Rahoton ya yi ikirarin cewa sabon farashin buhun simintin Ɗangote zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Octoba, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel