Shehu Sani Ya Yi Martani Kan Kwace Kujerun Yan Majalisar PDP Da Kotun Zabe Ta Yi a Jihar Filato

Shehu Sani Ya Yi Martani Kan Kwace Kujerun Yan Majalisar PDP Da Kotun Zabe Ta Yi a Jihar Filato

  • Sanata Shehu Sani ya yi martani ga tsige yan majalisar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Filato
  • Tsohon dan majalisar ya ce tsige yan majalisar PDP da aka yi na "daya daga cikin hukunce-hukunce masu ban tausayi da ban dariya”
  • Sani ya ce kada a yarda hukuncin ya yi tasiri saboda adalci ya fara ama tamkar wasan 'Ludo' a kasar nan

Tsohon sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya yi Allah wadai da tsige Honorable Beni Lar da sauran yan majalisar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da kotun zaben jihar Filato ta yi.

Sani ya bayyana tsige yan majalisar na PDP a matsayin "daya daga cikin hukunce-hukunce masu ban tausayi da ban dariya."

Shehu Sani ya yi watsi da tsige yan majalisar PDP da kotun zabe ta yi a Filato
Shehu Sani Ya Yi Martani Kan Kwace Kujerun Yan Majalisar PDP Da Kotun Zabe Ta Yi a Jihar Filato Hoto: Shehu Sani
Asali: Facebook

Bai kamata hukuncin ya yi tasiri ba

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar PDP Ya Gamu da Mummunan Hatsari, Mutum Huɗu Sun Ji Rauni

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) @ShehuSani, ya soki hukuncin kotun zaben kan hujjar cewa "jam'iyyarsu bata da tsari".

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon dan majalisar tarayya ya ce "Adalci yana zama tamkar wasan Ludo" kuma bai kata a bar shi ya yi tasiri ba.

"Tsige Honorable Beni Lar, dan majalisar wakilai da sauran yan majalisa daga jihar Filato da kotun zabe ta yi kan hujjar cewa "jam'iyyarsu bata da tsari" yana daga daga cikin hukunce-hukunce mafi tausayi da ban dariya a wannan kakar na hukunci masu ban mamaki da ban al'ajabi. Adalci ya fara zama wasan 'Ludo'. Wannan ba zai iya tasiri ba kuma kada a bari ya yi tasiri."

Kotun zabe ta kwace kujerun 'yan majalisar PDP uku a jihar Filato

Kara karanta wannan

Zuwan Wike Abuja: Jigon APC ya fadi babban abin da Wike zai yi a matsayin minista

Ku tuna cewa, kotun sauraron ƙararrakin zaben 'yan majalisun jiha da na tarayya ta ƙwace kujerun mambobin majalisar dokokin jihar Filato uku na jam'iyyar PDP.

Waɗanda Kotun ta tsige sun haɗa da, Remvyat Nanbol, mai wakiltar Langtang ta tsakiya, Agbalak Adukuchill, mai wakiltar mazabar Rukuba/Iregwe da Happiness Akawu da ke wakiltar Pengana a majalisar dokokin jihar.

A hukuncin da ta zartar a ranar Alhamis, kotun ta bayyana Daniel Ninbol Listic na jam’iyyar LP, Bako Ankala da Yakubu Sanda na APC da suka zo na biyu a matsayin wadanda suka yi nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel