Yan Bindiga Sun Harbi Daliban Kwalejin Kimiyya Da Ke Nasarawa 3, Sun Yi Garkuwa Da Mutum Daya

Yan Bindiga Sun Harbi Daliban Kwalejin Kimiyya Da Ke Nasarawa 3, Sun Yi Garkuwa Da Mutum Daya

  • Yan bindiga sun farmaki daliban kwalejin kimiyya da fasaha ta Isa Mustapha Agwai 1 da ke garin Lafia, jihar Nasarawa
  • Maharan sun harbi dalibai uku a yayin harin da ya gudana a ranar Litinin, 25 ga watan Satumba, kuma yanzu haka suna asibiti suna samun kulawar likitoci
  • Har wayau, yan bindigar sun yi garkuwa da wata dalibar aji biyu mai suna Ajoke zuwa wani waje da ba a san ko'ina bane

Jihar Nasarawa - Rahotanni sun kawo cewa tsagerun yan bindiga sun harbi daliban kwalejin kimiyya da fasaha ta Isa Mustapha Agwai 1 da ke garin Lafia, jihar Nasarawa.

Daily Trust ta rahoto cewa maharan sun kuma yi garkuwa da wata daliba mace wacce aka bayyana sunanta a matsayin Ajoke.

Yan bindiga sun harbi dalibai a jihar Nasarawa
Yan Bindiga Sun Harbi Daliban Kwalejin Kimiyya Da Ke Nasarawa 3, Sun Yi Garkuwa Da Mutum Daya Hoto: @FaridaAAsule
Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar Aminiya ta rahoto, Ajoke ta kasance dalibar mataki na biyu a bangaren kimiyyar gwaje-gwaje.

Kara karanta wannan

Karya da yaudara: Na hannun daman Atiku ya fadi karairayin Tinubu 10 tun hawansa mulki

An tattaro cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 08:00 n daren ranar Litinin, 25 ga watan Satumba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daliban da suka ji rauni daga harbin suna kwance a wani asibiti inda suke samun kulawar likitoci.

Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan Shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci jami’an tsaro da su ceto da sauran daliban jami’ar tarayya ta Gusau dayan bindiga suka sace a ranar Alhamis din da ta gabata.

Mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan Abuja cewa, Tinubu ya yi Allah-wadai da abin da ya faru na sace daliban.

Ya kara da cewa shugaban kasar ya ce babu wata hujja ta da’a ga irin wannan danyen aikin da aka yi wa wadanda ba su ji ba ba su gani ba, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

An tafka asara yayin da gobara ta lamushe fitaccen kamfanin robobi a jihar kasuwanci

Badaru Ya Karyata Jita-jitar Cewa Su Na Tattaunawa Da 'Yan Bindiga A Asirce

A wani labarin kuma, ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya musanta zargin tattaunawa da 'yan bindiga a sirrance.

Badaru ya bayyana haka ne yayin martani ga Gwamna Dauda Lawal kan zargin tattaunawa da 'yan bindigan ba tare da sanin gwamnatin jihar ba.

Ya yi watsi da jita-jitar inda ya ce Gwamnatin Tarayya ta himmatu wurin dakile matsalar tsaro a kasar, cewar Leadership.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel