Wasu Sun Siffanta Kansu da Karnuka Sun Yi Ganawa a Jamus, Sun Yi Ta Haushi Ga Juna Madadin Magana

Wasu Sun Siffanta Kansu da Karnuka Sun Yi Ganawa a Jamus, Sun Yi Ta Haushi Ga Juna Madadin Magana

  • Abin al’ajabi ba ya karewa a duniya yayin da wasu ma su son siffanta kansu da karnuka su ka gudanar da wata ganawa ta musamman a Jamus
  • Mutanen ma su kama da karnuka madadin magana da junansu yayin ganawar, an gano su su na haushi ga juna don tattaunawa
  • A kwanakin baya, wani dan kasar Japan, Toco ya kashe Naira miliyan 10 don sauya siffarshi zuwa ta kare tare da zuwa wurin karnuka don wasa

Berlin, Jamus – Wasu mutane da ke son kamanta kansu da karnuka sun taru don yin wata ganawa ta musamman.

A cikin wani faifan bidiyo da ya karade kafofin sadarwa, wadanda su ka halarci bikin madadin Magana da juna sun yi ta haushi ga junansu a matsayin magana.

Wasu ma su siffar kare sun gana a Jamus, sun yi ta haushi
Mutanen da su ka siffantu da kare kenan yayin wata ganawa. Hoto: Jam Press, I Want To Be An Animal.
Asali: Facebook

Meye mutane ke cewa kan bidiyon?

Kara karanta wannan

Gaskiya Kenan: ASUU Ta Yi Kakkausar Martani Kan Karin Kudin Jami'o'i, Ta Fadi Abin Da Zai Faru

Wannan lamari ya bai wa mutane da ke kallonsu a gefe mamaki da kuma abin al’ajabi, Legit ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kwanakin baya, wani mutum ya kashe akalla Naira miliyan 10.7 don sauya halittarsa zuwa ta kare.

Mutumin ya kashe makudan kudaden ne don cika burinsa na zama mai kama da kare musamman yanayin hakorarsa.

Kamar yadda New Yok Post ta tattaro mutanen da su ka sauya kamannin nasu sun sha suka daga mutane da dama.

Yayin da wasu ke cewa ya kamata a samu mai kula da dabbobi don su zo su gudanar da lamarin tare da daukar mataki akansu.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Martanin mutane kan wannan faifan bidiyo da ya karade kafar sadarwa:

Martanin mutane kan wannan faifan bidiyo da ya karade kafar sadarwa:

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Ware Naira Dubu 245 Ga Ko Wane Mai Bautar Kasa, Ya Yi Alkwari Ga Wasu Matasan

“Ban ga ko wane daya daga cikinsu ya na shinshina bindin dan uwanshi ba kamar karnuka,” cewar wani mutum.

Yayin da wani ya kara da cewa:

“Amma idan har sun siffanta kansu da karnuka, me ya sa su ka saka takunkumin fuska?”

Wani ya kashe N10m don siffanta kanshi da kare

A wani labarin, wani mutumin kasar Japan ya kashe makudan kudade don mayar da kanshi kamar kare tare da shiga bainar jama’a.

Mutum mai suna Toco ya ce a kullum burinsa shi ne ya zama kamar dabba kuma sanya rigar da ya yi da ta mayar da shi kamar kare ya cika masa burinsa.

Toco ya kuma fito bainar jama’a a karon farko yayin da mutane ke mamakin ganinshi ya na gaisawa da mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel