Alkawuran da Tinubu, Atiku da Wasu da ke Neman Takarar Shugaban Kasa Suka Fara Yi wa Talakawa

Alkawuran da Tinubu, Atiku da Wasu da ke Neman Takarar Shugaban Kasa Suka Fara Yi wa Talakawa

Yayin da ake dab da buga gangar zaɓen 2027, manyan ƴan siyasa da ke neman takarar shugaban ƙasa sun fara bayyana abin da za su yi wa talaka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Nigeria – A ƴan makonnin da suka gabata, an ji yadda Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi da Peter Obi suka yi ta magana a kan shirin da suka yi wa Najeriya.

Dukkaninsu ƴan jam'iyyar ADC ne da suka fara nuna sha'awar neman takarar kujerar da shugaba na yanzu, Mai girma Bola Ahmed Tinubu na APC ke ma.

Masu neman takara a 2027 sun fara yi wa talakawa romon baka
Tsofaffin ƴan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, Atiku Abubakar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Mister Peter Obi/Atiku Abubakar/Bayo Onanuga
Source: Twitter

Shi ma a ƙarshen mako, an ji shugaban yana bayyana irin ayyukan da zai yi wa ƴan Najeriya, musamman bayan abokan hamayyarsa sun yi magana.

Legit ta tattaro alkawarin da jagororin siyasa da suka hada da Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi da Peter Obi suka yi wa ƴan Najeriya.

Kara karanta wannan

Siyasar Arewa: Yusuf Buhari da ƴaƴan manyan mutane 4 da za su fito takara a 2027

Alkawarin manyan ƴan siyasa ga ƴan Najeriya

1. Bola Tinubu

Shugaba Bola Tinubu, a ranar Alhamis 16 ga watan Afrilu, 2026 ya sake jaddada aniyarsa na gina ƙasa mai ɗorewa, da ke zaune lafiya da wadata, inda ya tabbatar da cewa jin daɗin ƴan Najeriya shi ne babban abin da ya sa a gaba.

Bola Tinubu ya ce ba zai bar jama'ar Najeriya a kunci ba
Shugaban Najeriya na yanzu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Gwamnati ta wallafa a shafin yanar gizo cewa Tinubu ya ce an fara sauya tsarin siyasa da tattalin arziƙi da suka dade suna hana ƴan Najeriya samun wadata sannu a hankali ta hanyar daidaita tattalin arziƙi domin bai wa kowa damar shiga.

Shugaba Tinubu ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta mutunta ginshiƙan dimokuraɗiyya, daga ciki har da bin doka, raba iko tsakanin sassa, da kuma kare haƙƙin dukkan ƴan ƙasa.

2. Atiku Abubakar

A wata hira da Arise News, Abubakar ya ci gaba da sukar gwamnatin Shugaba Tinubu ta yanzu, inda ya bayyana ta a matsayin mafi muni da ya taɓa gani a Najeriya, tare da nuna matuƙar takaici kan yadda take gudanar da aiki.

Kara karanta wannan

Gabanin 2027, ADC ta fada wa Tinubu maganar da za ta jefa masa tsoron 'yan adawa

“Komai ba daidai ba ne. Gaskiya, a rayuwata, wannan ita ce gwamnatin da ta fi muni da na taɓa gani a wannan ƙasa. Ina matuƙar takaici.”
Atiku Abubakar ya ce tsaro ne zai zama mafi muhimmanci a gwamnatinsa idan ya ci zaɓe
Tsohon ɗan takarar Shugaban ƙasa Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Idan aka zaɓe shi, Atiku Abubakar ya ce babban abin da zai fara ba muhimmanci shi ne inganta tsaro, yana mai cewa babu wani shiri na tattalin arziƙi ko na gine-gine da zai yi aiki ba tare da tsaro ba.

3. Peter Obi

Jaridar Business Day ta ruwaito cewa yayin da gasar zaɓen 2027 ke fara ɗaukar harama, Peter Obi ya yi alkawarin bunƙasa dimbin arzikin noma na Arewacin Najeriya tare da mayar da shi sabon ginshiƙin tattalin arziƙin ƙasa.

Peter Obi ya ce zai mayar da hankali kan Arewa idan an zabe shi
Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi da ke son neman takarar shugaban ƙasa Hoto: Mister Peter Obi
Source: Twitter

Obi ya bayyana cewa babu wani ɗan takara da ke shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 da zai iya kai ga samar da shigen shirinsa a kan Arewacin Najeriya.

Ya jaddada cewa tsaro shi ne tushen duk wani ci gaba mai ma’ana, musamman a Arewa inda rashin tsaro ya kawo cikas ga noma da harkokin tattalin arziƙi.

4. Rotimi Amaechi

Jaridar Punch ta ruwaito tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce ƙwarewarsa a harkokin mulki da bunƙasa gine-gine na ba shi damar magance ƙalubalen Najeriya idan ya zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan

"Saura ƙiris": Trump ya faɗi lokacin kawo ƙarshen yaƙi da Iran

Rotimi Amaechi ya ce zai iya maganin matsalar Najeriya
Rotimi Amaechi da ke neman takarar shugaban Najeriya Hoto: Rotimi Amaechi
Source: Twitter

Amaechi, wanda ya bayyana hakan a shirin The Morning Brief na Channels Television a ranar Juma’a, 18 ga watan Afrilu, 2026 ya ce ya fahimci matsalolin ƙasar kuma yana da ikon magance su.

Ya ce:

“Shugaba Tinubu ba shi da ikon yin magana. Ya yi alkawarin wutar lantarki, ya ce idan bai samar da ita ba, kada a zaɓe shi. ‘Yan Najeriya na jiran su kaɗa masa ƙuri’a su fitar da shi."

Amaechi ya ƙalubalanci Tinubu

A baya, mun wallafa cewa tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, na daga cikin masu son samun takara a jam'iyyar ADC domin fafatawa da shugaban kasa Bola Tinubu.

Rotimi Amaechi ya fito ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan yadda tattalin arzikin kasar nan ya tabarbare yayin da jama'a ke kuka da kunci da suke ciki.

Tsohon Ministan a zamanin Muhammadu Buhari ya bayyana cewa 'yan Najeriya da dama sun kosa domin kawar da Shugaba Tinubu a zaben 2027 mai zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng