"Muna Zargin Akwai Wata Manaƙisa a Gobarar Kotun Koli" PDP Ta Maida Martani

"Muna Zargin Akwai Wata Manaƙisa a Gobarar Kotun Koli" PDP Ta Maida Martani

  • Jam'iyyar PDP ta maida martani kan ibtila'in gobara da ya ƙone wani sashi a Kotun ƙolin Najeriya
  • Kakakin PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce suna zargin akwai lauje cikin naɗi duba da manyan kararrakin da ke gaban Kotun
  • Ya buƙaci hukumomin tsaro su gudanar da bincike mai zurfi kuma su faɗa wa yan Najeriya duk abinda suka gano babu rufa-rufa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP ta nuna damuwa kan gobarar da ta tashi a kotun koli, inda ta bayyana hakan a matsayin abin tuhuma.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP ta kasa, Debo Ologunagba, shi ne ya bayyana damuwar jam’iyyar a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ranar Litinin.

PDP ta maida martani kan gobarar wani sashi a Kotun koli.
"Muna Zargin Akwai Wata Manaƙisa a Gobarar Kotun Koli" PDP Ta Maida Martani Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Jam'iyyar PDP ta maida raddi

A sanarwan wacce PDP ta wallafa a shafinta na manhajar X ranar 25 ga watan Satumba, 2023, Mista Ologunagba ya ce:

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Yi Magana Mai Kyau Bayan Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Da Ya Samu a Zaɓen 2023

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Jam’iyyar PDP ta damu matuka kan gobarar da ta auku, musamman ganin yadda jama’a ke fargabar yiwuwar kai harin kone-kone da nufin gurgunta da kuma hana kotun koli ta gudanar da ayyukanta yadda ya kamata."
"Musamman idan aka yi la'akari da manyan kes ɗin da ke gaban Kotun Ƙoli a halin yanzu, ciki harda ƙarar zaben shugaban ƙasa."
"Jam’iyyarmu na bukatar a gaggauta gudanar da cikakken bincike mai zurfi kan barkewar gobarar da nufin bankado waɗanda suka kunna ta da masu zagon kasa a lamarin."

Muna son a fallasa sakamakon binciken kowa ya gani - PDP

Jam'iyyar PDP ta buƙaci a bayyana sakamakon binciken ga jama'a domin tana zargin akwai lauje ciki naɗi duba da yadda a baya gwamnatin APC ke danne abinda aka gano.

"PDP tana jaddada buƙatar fallasa duk abinda binciken ya bankaɗo a bainar jama'a ba kamar yadda idan aka yi gobara a ma'aikatu da hukumomi gwamnatin APC ke rufa-rufa ba a baya"

Kara karanta wannan

Gobara Ta Laƙume Takardun Ƙarar Zaben Shugaban Ƙasa a Kotun Ƙoli? Gaskiya Ta Bayyana

"PDP na kira ga FG ta kara tsaurara matakan tsaro a kewayen Kotun Koli, sannan a baiwa ‘yan Najeriya tabbacin kare wasu muhimman takardu da kayan aiki a Kotun musamman a wannan mawuyacin lokaci.”

Muna da Kwararan Hujjojin da Zamu Tona Muku Asiri, Zamfara Ta Maida Martani Ga FG

A wani rahoton kuma Gwamna Dauda Lawal ya sake maida zazzafan martani ga gwamnatin tarayya kan tattaunawar sulhu da 'yan bindiga a Zamfara.

Tun da fari, gwamnan ya ce gwamnatin tarayya ta shiga tattaunawa da yan bindiga, lamarin da ya yi wa FG zafi har ta maida masa raddi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel