Kano Ta Dauki Zafi, Gwamna Abba Ya Yi Kalaman da Ake Zargin Ya Saki Matarsa
- Ana zargin gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya saki matarsa ta biyu Zainab Kwankwaso, ’yar tsohon ubangidansa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
- Gwamnan ya yi wasu kalamai da ke nuna mutuwar auren a ranar Litinin yayin ganawa da ’yan fansho a gidan gwamnatin Kano
- Ya kuma nuna cewa yana iya sake aure a nan gaba, tare da roƙon jama’a su yi masa addu’ar samun mace ta gari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi wasu kalamai a bainar jama’a da ke nuna cewa aurensa da Zainab Musa Kwankwaso, ya mutu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake jawabi ga ’yan fansho a wani taro da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano, inda ya yi amfani da barkwanci da salon magana na misalai wajen sanar da batun.

Source: Facebook
Kalaman da Gwamna Abba ya yi
Daily Trust ta rahoto cewa yayin da yake magana da Hausa, Gwamna Abba ya kwatanta matsayin aurensa da rage masa matsayi a aikin soja, inda ya ce ya koma daga matsayin “kofur” zuwa “konstabul” saboda yanzu yana da mata ɗaya ne kawai.
"Wannan waka da aka yi ta falle daya, sai na tuna lokacin muna matasa samari, ana kiranmu da konstabul watau falle daya, da muka tashi muka girma, sai Allah Ya ba mu iko muka zama kofur, watau falle biyu.
"Yau ana kiranmu falle biyu, to na zama gwamna, kamata ya yi na wuce zuwa falle uku amma saboda yanayin aikin hidimtawa al'umma, sai muka hakura muka zauna da falle biyu.
"A yan kwanakin da suka wuce sai muka ga ana so ko koma konstabul watau da guda daya, ina kara gode wa al'ummar jihar Kano da suke ta bamu shawarwari mu tsaya a falle biyu, amma a yanzu mun karbi falle dayan."
- In ji Abba Kabir Yusuf.
Abba ya nuna alamun zai kara aure
Gwamna Abba bai bayyana cewa ya saki Zainab kai tsaye ba, inda ya kara da cewa wanda ya fahimci kalamansa ya fahimta, wanda kuma bai fahimta ba shikenan.
Ya kar da cewa:
"Wanda ya gane ya gane, wanda kuma bai gane ba, ba zai gane ba. Gwamna ya yarda ya saki wannana abar, takarda ce ko? Gwamna ya bayar.
"Ku taya gwamna addu'a cikin wadanda za su nema idan mun saki talla a jaridu, Allah Ya hada mu da na gari masu mutunci, wadanda suka san darajar falle biyu.
Ya kuma roƙi mazauna jihar da su yi masa addu’ar samun matar da ta dace, yana mai cewa ya gamsu da matakin da aka ɗauka, kuma yana roƙon Allah Ya shiryar da shi zuwa ga mutanen kirki.
Jawabin gwamnan ya zo ne kwanaki biyu kacal bayan rahotannin cewa Zainab Musa Kwankwaso, wadda aka ce ita ce matarsa ta biyu, ta garzaya wata babbar kotun shari’a da ke Gudu a Abuja, domin neman a raba aurensu. Iko

Kara karanta wannan
Babbar magana: Matar Gwamna Abba na jihar Kano ta nemi saki a kotu, ta fadi dalili
Ya zuwa yanzu, iyalan Kwankwaso ko ofishin gwamnan ba su fitar da cikakkiyar sanarwa don tabbatar da sakin ba amma dai kalaman Abba sun bayyana cewa auren ya ƙare.
Asali: Legit.ng

