Sabon Tsarin da Kwankwaso Yake So a Yi Amfani da Shi a Zaben Shugaban Kasa a Najeriya
- Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC, Rabiu Kwankwaso, ya ce ya kamata a gyara kundin tsarin mulkin Najeriya
- Kwankwaso ya yi zargin cewa ana hana jam’iyyun adawa gudanar da kamfen cikin sauƙi a wasu jihohi, tare da ambaton Benue, Cross River da Legas
- Tsohon gwamnan na Kano ya nuna damuwa kan cire sunan ɗan takarar gwamnan Kano na NDC, Aminu Abdussalam, daga jerin sunayen INEC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira da a sake duba kundin tsarin mulkin Najeriya nan gaba.
Kwankwaso ya ce ya kamata a tabbatar da cewa duk wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa ya samu aƙalla 50% cikin 100% na ƙuri’un da aka kaɗa.

Kara karanta wannan
Peter Obi ya shirya share hawayen 'yan Arewa, ya gano hanyar magance matsalar yankin

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce ya bayyana hakan ne ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamban 2026 yayin bikin yaye ɗalibai karo na biyar na jami’ar Skyline University Nigeria da ke Kano.
Kwankwaso ya yi tsokaci kan zaɓen 2023
Tsohon gwamnan jihar Kano ya yi nuni da zaɓen shugaban ƙasa na 2023, inda ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya samu kusan ƙuri’u miliyan 8.7 daga cikin kusan miliyan 24 da aka kaɗa.
Ya ce adadin ya kai kusan 34% ko 35% cikin 100% na ƙuri’un da aka kaɗa, amma idan aka kwatanta da masu rajistar zaɓe miliyan 93 a Najeriya, ya kai kusan 9% cikin 100%.
A kalamansa, Kwankwaso ya ce:
"Ina ganin nan gaba akwai buƙatar mu sake duba kundin tsarin mulkinmu, domin tabbatar da cewa shugaban ƙasa ya samu aƙalla 50% cikin 100% ko fiye na ƙuri’un da aka kaɗa kafin ya shiga fadar shugaban ƙasa, ba 34% ko 35% cikin 100% ba.”
Ya zargi wasu gwamnonin da hana adawa kamfen
Kwankwaso ya kuma nuna damuwa kan abin da ya bayyana a matsayin ƙarin zafafa siyasa a Najeriya.
Ya yi zargin cewa ana hana jam’iyyun adawa damar gudanar da kamfen a wasu jihohi, inda ya ce hatta rataya fastoci da tutocin kamfen ya zama abu mai wahala a wasu yankuna.
A cewarsa, wasu gwamnonin jihohi na ɗaukar nauyin wasu mutane domin hana jam’iyyun adawa gudanar da harkokin yaƙin neman zaɓensu.
Ya ambaci jihohin Benue, Cross River da Lagos a matsayin wuraren da ya ce jam’iyyun adawa suka fuskanci hare-hare da wasu matsaloli yayin gudanar da kamfen.
Kwankwaso ya nuna damuwa kan INEC da kotuna
Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasar ya kuma nuna damuwa kan yadda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ɓangaren shari’a ke tafiyar da wasu batutuwan zaɓe.
Ya kawo batun cire sunan ɗan takarar gwamnan Kano na NDC, Comrade Aminu Abdussalam, daga wani sabon jerin sunayen ’yan takara da hukumar ta fitar.
Ya ce Abdussalam ya cika dukkan sharuddan tsayawa takara, kuma sunansa tare da na NDC sun bayyana a jerin farko da INEC ta wallafa.
Sai dai ya ce daga baya hukumar ta cire sunayen a wani sabon jerin da ta fitar ranar 10 ga Oktoban 2026.
Kwankwaso ya bayyana cewa lokacin da jam’iyyar ta nemi ƙarin bayani daga INEC, hukumar ta ce akwai shari’a da ake yi kan batun.

Source: Facebook
Kwankwaso ya yi zargi kan gwamnatin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jinkirta karɓar haraji bisa sababbin dokokin haraji.
Kwankwaso ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya ta ɗauki wannan mataki ne saboda fargabar cewa aiwatar da dokokin na iya jawo mata matsala a babban zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng

