Siyasa Ta Yi Zafi: Kwankwasiyya Ta Yi Martani Mai Zafi ga Gwamnatin Abba

Siyasa Ta Yi Zafi: Kwankwasiyya Ta Yi Martani Mai Zafi ga Gwamnatin Abba

  • Kwankwasiyya ta zargi gwamnatin Kano da mayar da batun harin da aka ce an kai wa ayarin motocin Kwankwaso siyasa
  • Ƙungiyar ta soki Kwamishinan Yaɗa Labarai, Sanusi Bature Dawakin Tofa, kan neman hotuna da bidiyo maimakon barin jami’an tsaro su gudanar da bincike
  • Ta buƙaci rundunar ’yan sandan Kano ta binciki lamarin, ciki har da zargin lalata motoci da jikkata wasu mambobin tawagar Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Ƙungiyar Kwankwasiyya ta zargi gwamnatin Jihar Kano da siyasantar da rahoton harin da aka ce an kai wa ayarin motocin jagoranta, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Ƙungiyar ta jaddada cewa Jihar Kano mallakar dukkan mazaunanta ce, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasar da suke goyon baya ba.

Kwankwasiyya ta soki gwamnatin Abba Kabir
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Mai magana da yawun ƙungiyar, Dr Habibu Sale Mohammed, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamban 2026, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta fadi karyar da ta ce an shirya kan kai wa Kwankwaso hari

Kungiyar ta ce gwamnati na da alhakin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, kuma bai kamata bambancin siyasa ya zama sanadin tauye musu tsaro da haƙƙoƙinsu na asali ba.

Dr. Habibu Sale ya ce sun mayar da martani ne kan rahoton harin da aka ce an kai wa ayarin motocin Kwankwaso yayin wani taron siyasa a ƙaramar hukumar Bichi ranar Lahadi.

Zargin siyasantar da lamarin

Kwankwasiyya ta soki gwamnatin jihar bisa watsi da lamarin, inda ta bayyana shi a matsayin ƙirƙirarren labari tare da zargin ƙungiyar da ƙirƙirar zargin domin neman tausayi a wajen jama’a.

Ƙungiyar ta kuma yi suka ga Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa, bisa buƙatar hotuna da bidiyoyin abin da ya faru maimakon barin jami’an tsaro su gudanar da bincike.

Ta tambayi dalilin da ya sa ya kamata waɗanda suka ce an kai musu hari su gabatar da hujjoji kafin gwamnati ta nuna damuwa kan tsaronsu.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya shirya share hawayen 'yan Arewa, ya gano hanyar magance matsalar yankin

A cikin sanarwar, ƙungiyar ta ce:

"Kano mallakar dukkan al’ummarta ce, ba wai kawai waɗanda ke riƙe da mukaman gwamnati ba. Tsaronta, zaman lafiyarta da ’yancin dimokuraɗiyyarta nauyi ne na kowa, wanda bai kamata a sadaukar da shi saboda siyasar jam’iyya ba.”

Kira ga ’yan sanda su gudanar da bincike

Ƙungiyar ta ce alhakin binciken zargin aikata laifi ya rataya ne a wuyan jami’an tsaro, ba waɗanda suka ce an kai musu hari ba.

Ta kuma zargi kwamishinan da yanke hukunci kan lamarin ba tare da gabatar da sakamakon wani binciken ’yan sanda ba, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Saboda haka, ta buƙaci rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta gudanar da cikakken bincike domin gano abin da ya faru a Bichi da kuma tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da hannu.

Haka kuma, ta nemi a binciki zargin lalata motoci da kuma jikkata wasu daga cikin mutanen da ke cikin tawagar Kwankwaso.

An buƙaci Abba ya tabbatar da tsaro

Kara karanta wannan

Dambarwar neman sakin matar Gwamna Abba ya jefa wasu mutane a matsala, an samu bayanai

Kwankwasiyya ta buƙaci Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fifita tsaro da zaman lafiya fiye da bambancin siyasa, tare da tabbatar da kare dukkan jam’iyyun siyasa, ’yan takara, jami’an kamfen da magoya bayansu a faɗin jihar.

Ta yi gargaɗi kan amfani da barazana wajen tsoratar da ’yan adawa, tana mai cewa dole ne a ba su damar gudanar da harkokin siyasa bisa doka ba tare da fargabar cin zarafi ko tashin hankali ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa:

“Fafatawar siyasa ba yaƙi ba ce, kuma kasancewa ɗan adawa ba laifi ba ne.”

Ƙungiyar ta ce tana nan daram kan shiga harkokin siyasa cikin lumana, amma hakan bai kamata a ɗauka a matsayin amincewa da tsoratarwa ko rashin hukunta masu laifi ba.

Ta kuma buƙaci gwamnatin jihar ta bar jami’an tsaro su gano gaskiyar abin da ya faru kafin ta riƙa fitar da sanarwa kan lamarin.

Kwankwasiyya ta yi wa Gwamna Abba martani
Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

An yi zargi kan Kwankwaso

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya yi zargi kan madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Bayo Onanuga ya zargi tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, da ƙarfafa magoya bayansa su shirya makamai gabanin babban zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng