Abin Jimami: Gobara Ta Lakume Ango da Amarya Suna cikin Barci

Abin Jimami: Gobara Ta Lakume Ango da Amarya Suna cikin Barci

  • Sikiru Habib da matarsa Ramlat Lawan sun rasu bayan gobara ta tashi a ɗakinsu da ke Anguwan Miyango, Bukuru, Jihar Plateau
  • Gobarar ta tashi da misalin ƙarfe 2:30 na daren ranar Asabar, lokacin da ma’auratan ke barci a cikin ɗakinsu
  • An garzaya da ma’auratan Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH), inda aka ce ango ya rasu ranar Lahadi, amarya kuma ranar Litinin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Wata gobara da ta tashi a gidan wasu sababbin ma’aurata, Sikiru Habib da matarsa Ramlat Lawan, ta yi sanadin mutuwarsu a Anguwan Miyango, Bukuru, ƙaramar hukumar Jos South ta Jihar Plateau.

Mazauna yankin sun bayyana lamarin a matsayin babban bala’i, inda suka ce gobarar ta kama ɗakin ma’auratan da sanyin safiyar Asabar, da misalin ƙarfe 2:30 na dare.

Ma'aurata sun rasu a Plateau
Sikiru Habib da Ramlat wadanda suka rasu sakamakon gobara Hoto: Mustapha Ibrahim
Source: Facebook

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa gobarar ta tashi ne a lokacin da ma’auratan ke barci a cikin ɗakinsu.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya shirya share hawayen 'yan Arewa, ya gano hanyar magance matsalar yankin

Yadda gobarar ta tashi

Wasu mazauna yankin sun yi zargin cewa tashin wutar lantarki mai ƙarfin gaske ne ya haddasa gobarar.

Sai dai har yanzu babu wata sanarwa a hukumance da ta tabbatar da wannan zargi ko musabbabin tashin gobarar.

Injiniya Lawal Suleiman, wanda maƙwabcin mamatan ne, ya bayyana lamarin a matsayin abin ban tsoro.

Ya ce angon ya rasu ne ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamban 2027 yayin da amaryarsa ta rasu ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamban 2026 bayan an kai su asibiti domin samun kulawar likitoci.

Ƙoƙarin ceto ma’auratan

Injiniya Lawal Suleiman ya bayyana cewa lamarin ya ƙara muni ne bayan ƙofar ɗakin ta ƙi buɗewa, lamarin da ya sa ma’auratan suka makale a ciki yayin da wutar ke ci gaba da yaɗuwa.

Makwabta, musamman matasa maza, sun garzaya wurin domin ƙoƙarin ceto ma’auratan daga cikin ɗakin.

Ya ce daga bisani sun samu damar shiga ɗakin ta taga, inda suka fitar da ma’auratan kafin jami’an kashe gobara su isa wurin domin ba da agajin gaggawa.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kwankwaso ya fito ya gayawa duniya wani halin Peter Obi

Bayan fitar da su, an garzaya da sababbin ma’auratan zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH), domin samun kulawar likitoci.

Sai dai duk da ƙoƙarin ceto rayukansu da kuma kulawar da suka samu a asibitin, angon ya rasu ranar Lahadi, amaryarsa kuma ta rasu ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamban 2026.

Gobara ta kashe ma'aurata a Plateau
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gobara ta kashe uwa da 'ya'yanta

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata mata da ’ya’yanta hudu sun mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a gidansu da ke Okochiri, karamar hukumar Okrika a Jihar Rivers.

Lamarin ya faru ne da safe, inda aka gano gawarwakin matar da ’ya’yanta bayan jami’an da suka isa wurin sun tarar da gidan ya kone.

Wani da ya san abin da ya faru, wanda ya nemi a boye sunansa, ya ce gobarar ta tashi ne lokacin da wani mutum ke kokarin zuba man fetur a cikin jarka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng