Tashin Hankali: Gobara Ta Kama a Katafariyar Ma'ajiyar Babban Dan Kasuwa a Jihar Kaduna

Tashin Hankali: Gobara Ta Kama a Katafariyar Ma'ajiyar Babban Dan Kasuwa a Jihar Kaduna

  • Gobara ta kama a ma’ajiyar kayayyaki ta fitaccen dan kasuwa mai sayar da tayoyi, Alhaji Yakubu Ibrahim, da ke kan titin Katsina a cikin birnin Kaduna
  • Rahoto ya nuna cewa gobarar ta lalata tayoyi da sauran kayan haɗin motoci da dama, inda aka kiyasta asarar ta kai miliyoyin nairori
  • Jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kaduna sun samu nasarar shawo kan lamarin tare da hana wutar yaɗuwa zuwa shaguna da gine-ginen da ke kusa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Wata gobara ta kama ma’ajiyar kayayyaki ta fitaccen dilan tayoyi, Alhaji Yakubu Ibrahim, da ke kan titin Katsina a cikin birnin Kaduna, lamarin da ya jefa ’yan kasuwa da mazauna yankin cikin firgici.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a ma’ajiyar da ke kusa da titin Lagos, wani babban yankin kasuwanci a ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa.

Kaduna.
Taswirar jihar Kaduna da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Leadership ta ce shaidun gani da ido sun ce gobarar ta tashi da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, inda ta bazu cikin sauri a ma’ajiyar, ta ƙone tayoyi da sauran kayan haɗin motoci da aka ajiye a wurin.

Yadda aka yi kokarin kashe gobarar

Ma’ajiyar ta Alhaji Ibrahim ce, wanda dillali ne da aka amince da shi wajen kasuwancin tayoyin kamfanin Michelin. Rahotanni sun ce akwai ɗaruruwan tayoyi da wasu kayayyaki masu daraja a cikin ma’ajiyar.

Gobarar, wadda abubuwa masu saurin kamawa da wuta da ke cikin ma’ajiyar suka ƙara rura mata wutar, ta gagari mazauna yankin da ’yan kasuwa da farko. Hakan ya sa aka kira hukumar kashe gobara ta jihar Kaduna domin neman agaji.

Hayaki mai yawa da ke tashi daga ma’ajiyar ya jefa yankin cikin rudani, yayin da ’yan kasuwa da mazauna wurin ke ƙoƙarin ceto kayansu tare da hana wutar yaɗuwa zuwa shaguna da gine-ginen da ke maƙwabtaka da wurin.

Sai dai jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kaduna sun isa wurin tare da shawo kan lamarin, inda suka hana wutar ci gaba da yaɗuwa.

An tafka asarar miliyoyin Naira

A lokacin kammala wannan rahoto, jami’an kashe gobara na ci gaba da aiki a wurin domin kashe sauran harshen wutar da kuma tabbatar da cewa babu sauran garwashin da zai iya sake tayar da gobarar.

An ruwaito cewa mazauna yankin da ’yan kasuwa sun yi nasarar ceto wasu tayoyi kafin wutar ta cinye su.

Duk da cewa har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba, an kiyasta asarar dukiyoyin da ta haddasa ta kai miliyoyin Baira. Ba a samu rahoton rasa rayuka ba a lokacin kammala rahoton.

A halin da ake ciki, jami’an ’yan sanda daga sashen Magaji Gari sun isa wurin domin tabbatar da zaman lafiya da kuma hana ɓata-gari amfani da lamarin wajen satar kaya daga shaguna da ma’ajiyoyi.

Wuta ta kona mutane a Edo

Kun ji cewa ana fargabar mutane da dama sun mutu da wata tankar mai ta fashe a kan titin Benin-Lagos kusa da Oluku a birnin Benin na Jihar Edo.

An ce mai ya kwarara daga tankar bayan ta faɗi, lamarin da ya jawo mutane suka yi tururuwa domin kwasar man fetur kafin ta kama da wuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262