An Hango Abin da Zai Faru idan Aka Yi Wa 'Yan Najeriya Karfa Karfa kan Tinubu a 2027

An Hango Abin da Zai Faru idan Aka Yi Wa 'Yan Najeriya Karfa Karfa kan Tinubu a 2027

  • Timi Frank ya yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na tilasta wa Shugaba Tinubu lashe zaɓen 2027 zai iya jefa Najeriya cikin rikici
  • Ya yi kira ga shugaban ƙasar da ya janye burinsa na neman wa’adi na biyu, tare da tabbatar da zaɓe mai gaskiya da adalci
  • Frank ya ce ihun da aka yi wa Tinubu a Abuja da kuma abubuwan da suka faru bayan gangamin APC a Jos sun nuna rashin jin daɗin wasu ’yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin kakakin yaɗa labarai na jam’iyyar APC na ƙasa, Timi Frank, ya yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na tilasta wa Shugaba Bola Tinubu komawa kan mulki a zaɓen 2027 na iya jefa Najeriya cikin rikici.

Frank, wanda shi ne jakadan United Liberation Movement for West Papua (ULMWP) a Gabashin Afirka da Gabas ta Tsakiya, ya ce ’yan Najeriya ba za su amince da sakamakon zaɓen da ya saɓa wa zaɓin da suka yi ta hanyar ƙuri’unsu ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kira ruwa, Dino Melaye ya yi masa tatas kan zaben 2027

An bukaci Tinubu ya hakura da tazarce
Shugaba Bola Tinubu da tsohon kakakin jam'iyyar APC, Timi Frank Hoto: @OfficialABAT, @RealTimiFrank
Source: Twitter

A cewarsa, bai kamata a ayyana wani ɗan takara a matsayin wanda ya lashe zaɓe alhali jama’a sun san ba su zaɓe shi ba, cewar rahoton jaridar Vanguard.

“’Yan Najeriya ba za su amince da yanayin da za a ayyana wani a matsayin wanda ya yi nasara alhali jama’a sun san ba su zaɓe shi ba. Kada su jefa ƙasar cikin rikici ta hanyar ƙoƙarin tilasta shi ga mutane.”

Ya bukaci Tinubu ya janye burin tazarce

Frank ya yi kira ga shugaban ƙasar da ya ajiye burinsa na sake tsayawa takara, tare da tabbatar da cewa za a gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci.

"Duk wanda ya yi nasara, ya kamata a bar shi ya zama zaɓin al’umma.” In ji shi.

Tsohon kakakin APC ya kuma nuna damuwa kan zargin cewa wasu ’yan siyasa na ƙoƙarin yin magudi ko katsalandan a tsarin zaɓe.

Ya yi tsokaci kan ihun da aka yi wa Tinubu

Kara karanta wannan

Jigo a ADC ya gano abin da Tinubu ke fargaba kan zaben 2027

Frank ya bayyana zanga-zangar da wasu mutane suka yi wa Tinubu bayan kammala sallar da aka gudanar a Masallacin Shehu Shagari da ke Area 1, Garki, Abuja, ranar Juma’ar da ta gabata a matsayin alamar ƙaruwa da rashin gamsuwa da gwamnatin.

Rahotan The Punch ya nuna cewa wasu masu zanga-zanga sun yi wa shugaban ƙasar ihu, suna rera kalmar “Ba ma yi” bayan sallar.

A wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, an ga wasu daga cikinsu suna cire fastoci da allunan tallan kamfen ɗin Tinubu tare da lalata su a wasu sassan Area 1.

Sai dai Frank ya soki masu zanga-zangar kan zaɓin lokacin ibada domin bayyana fushinsu. Ya kuma yaba wa jami’an tsaron shugaban ƙasa bisa kare lafiyarsa da kuma shawo kan lamarin ba tare da barin rikicin ya ƙara ta’azzara ba.

Duk da haka, ya bukaci Tinubu ya fahimci muhimmancin abin da ya faru da kuma sakon da jama’a ke aikawa.

Frank ya yi magana kan rashin jin daɗin jama’a

“Kin amincewa da shi ya kasance a bayyane kuma babu shakka. Babu wani shugaban Najeriya da aka taɓa kunyatawa a bainar jama’a irin wannan.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An fallasa shirin tafka magudi a babban zaben 2027

“Yadda ’yan Najeriya suka nuna rashin amincewarsu da shi yana da ma’ana sosai. Amma idan ya yanke shawarar ci gaba da takararsa kuma ya sha kaye, ya kamata ya shirya karɓar sakamakon kamar yadda tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya yi.” In ji shi.
Timi Frank ya ba Tinubu shawara
Shugaban kasa Bola Tinubu a wajen yakin neman zabe Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tinubu ya kawo tsarin samar da tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamitin kamfen din shugaban kasa na jam’iyyar APC (APC-PCC) ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na shirin samar da sabon tsarin dabarun yaƙi da matsalar tsaro na tsawon shekaru biyar.

Kwamitin ya kuma bayyana cewa Tinubu ya amince da ɗaukar ƙarin jami’an tsaro 78,000, domin ƙarfafa ayyukan sojoji da ’yan sanda wajen magance matsalar tsaro a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng