Tinubu Ya Fitar da Sabon Tsarin Tsaro da zai Kawo Zaman Lafiya a Shekara 5

Tinubu Ya Fitar da Sabon Tsarin Tsaro da zai Kawo Zaman Lafiya a Shekara 5

  • Jam’iyyar APC ta ce Shugaba Bola Tinubu ya kammala shirin tsaro na shekara biyar da nufin kawo karshen matsalar rashin tsaro a Najeriya
  • Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC ya yi ikirarin cewa sojoji sun kashe ’yan ta’adda sama da 15,000 cikin shekara uku
  • Shirin ya kunshi kara yawan sojoji da ’yan sanda, fadada cibiyoyin horas da dakarun tsaro da kuma inganta amfani da bayanan sirri da fasaha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ta jam’iyyar APC ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kammala wani sabon shirin tsaro na shekara biyar da aka tsara domin kawo karshen matsalar rashin tsaro.

Majalisar ta ce shirin zai karfafa tsarin tsaron kasar, inganta ayyukan sojoji da kuma tabbatar da hadin gwiwa wajen tinkarar sabbin barazanar tsaro.

Kara karanta wannan

Tinubu ya leƙo babbar matsalar ƴan Plateau, ya ɗauka masu alƙawari

Shugaba Bola Tinubu da jami'an tsaro
Hafsohsin tsaro da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

A sakon da Bayo Onanuga ya wallafa a Facebook ya ce mai magana da yawun kwamitin, Dele Alake, ne ya bayyana hakan a ranar 15 ga Nuwamba, 2026.

Me shirin tsaron Tinubu ya kunsa?

A cewar sanarwar, shirin zai samar da tsarin gudanar da ayyukan tsaro na dogon lokaci, ta yadda za a daidaita bukatun tsaro, ayyukan soji, bunkasa kayan aiki da kashe kudi da kalubalen da Najeriya ke fuskanta.

APC ta ce shirin zai mayar da hankali kan amfani da bayanan sirri, fasahar zamani da matakan rigakafi wajen yaki da ta’addanci, ’yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran laifuffuka.

Sanarwar ta kuma yi ikirarin cewa a cikin shekaru uku da gwamnatin Tinubu ta yi, sojoji sun kashe sama da ’yan ta’adda 15,000 da suka hada da mayakan Boko Haram da ’yan bindiga.

Haka kuma, ta ce mayakan Boko Haram da wadanda suke dogaro da su sama da 130,000 sun mika wuya ta hanyar shirin Operation Safe Corridor na gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kwantar da hankulan yan Najeriya kan yadda za a gudanar da zaben 2027

Tinubu zai kara yawan sojoji

Kwamitin ya bayyana cewa Tinubu ya amince da kafa sababbin rundunonin soji guda hudu tare da sake fasalin wasu cibiyoyin soji domin fadada ayyukansu da ba su damar kai dauki cikin gaggawa.

Haka zalika, shugaban kasar ya amince da kafa wasu sababbin cibiyoyin horas da sojoji guda biyu a Osogbo da ke jihar Osun da Amasiri-Edda a jihar Ebonyi.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a wajen kamfen. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sanarwar ta ce kowace cibiyar na da damar horas da sabbin sojoji 6,000 a lokaci guda, wanda ya kai jimillar mutum 12,000.

Rahoton Punch ya nuna cewa gwamnatin Najeriya ta ce a yanzu haka, an ce sabbin sojoji 5,210 na samun horo a cibiyar Osogbo.

Baya ga haka, Tinubu ya amince da daukar karin sojoji 28,000 da kuma ’yan sanda 50,000 domin karfafa jami’an tsaron kasar da inganta ayyukansu.

An karfafa tsaro a Katsina

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta kaddamar da jami’an tsaron daji 1,008 domin karfafa tsaro a dazuzzuka da kuma dakile ayyukan ’yan bindiga, ’yan ta’adda da masu satar shanu.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yaye jami’an tsaron daji 1008 a Katsina, ya fadi aikin da za su yi

Gwamna Dikko Radda ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye jami’an, inda ya bukace su da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da kishin kasa.

Ya ce jami’an za su hada kai da mambobin Rundunar Tsaron Al’umma ta jihar guda 3,000, da CJTF, jami’an sa-kai da mafarauta domin kare dazuzzuka da sauran wuraren da ke fama da matsalar tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng