Yadda Fusatattun Matasa Suka So Lakadawa Rarara Duka kan Tallata Tinubu

Yadda Fusatattun Matasa Suka So Lakadawa Rarara Duka kan Tallata Tinubu

  • Shahararren mawaƙin jam’iyyar APC, Dauda Kahutu Rarara, ya tsallake wani hari da ake zargin wasu matasa sun yi ƙoƙarin kai masa a Abuja
  • Lamarin ya faru ne a Monaliza Park yayin da Rarara ke ƙoƙarin gabatar da wata waƙa da ke nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu
  • Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun shiga tsakani tare da fitar da mawaƙin daga wurin, sai dai har yanzu babu bayanin hukuma kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shahararren mawaƙin APC, Dauda Kahutu Rarara, ya tsallake wani hari bayan wasu matasa sun nuna adawa da waƙar da ya yi ƙoƙarin gabatarwa domin nuna goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Rarara dai ya kasance daga cikin manyan masu tallata shugaba Bola Tinubu da 'yan takarar APC a Najeriya.

Kara karanta wannan

Siyasa ta ɗauki zafi, 'yan daba dauke da bindigu sun buɗe wa magoya bayan PDP wuta

Rarara a wajen taro
Dauda Rarara sanye da hula mai alamar tallata Bola Tinubu. Hoto: Dauda Kahutu Rarara
Source: Facebook

Leadership ta wallafa cewa lamarin ya faru ne a daren 1 ga Oktoba a Monaliza Park da ke Abuja, yayin wani taron bikin ranar samun ’yancin Najeriya.

Matasa sun hana Rarara waka

Rahotanni da ke yawo a kafafen sada zumunta sun ce Rarara yana kan dandali ne lokacin da wasu matasa suka nuna rashin amincewa da waƙar da yake shirin rerawa.

Lamarin ya ƙara tsananta yayin da masu zanga-zangar suka yi ta ihu tare da jefa abubuwa zuwa wajen dandalin, lamarin da ya tilasta wa mawaƙin dakatar da wasan.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro da ke wurin sun shiga tsakani domin kare Rarara tare da fitar da shi daga wurin.

An harba barkonon tsohuwa

A cewar rahotannin da ke yawo, jami’an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da harbe-harben gargadi domin tarwatsa taron bayan rikicin ya ƙara tsananta.

Lamarin ya haifar da firgici a wurin, inda wasu daga cikin mahalarta taron suka gudu yayin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin dawo da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Atiku ya fusata mutanen Tinubu, sun yi masa raddi mai zafi

Sai dai babu wani rahoto tabbatacce da ya nuna cewa an samu rauni ko kuma an kama wasu mutane dangane da rikicin har zuwa lokacin da aka wallafa rahotannin.

Motocin shugaba Bola Ahmed Tinubu
Motocin tallata Bola Tinubu a Nasarawa. Hoto: Gov Abdullahi A Sule Mandate
Source: Facebook

Wannan rikici ya faru ne a daidai lokacin da ake ƙara samun korafe-korafe kan tsadar rayuwa, hauhawar farashin abinci da sufuri da kuma matsin tattalin arziki da ake fuskanta.

Ga bidiyon abin da aka ce ya faru a wajen kamar yadda Sulaiman Uwaisu Idris ya wallafa a X:

Shugaban APC ya yi barazana

A wani labarin, kun ji cewa shugaban APC na Jihar Edo, Jarrett Tenebe, ya yi magana kan shirin jam’iyyar na samar wa Shugaba Bola Tinubu ƙuri’u miliyan 2.5 daga jihar a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Tenebe ya bayyana haka ne a Benin City yayin wani taron magoya bayan APC, bayan zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a jihar.

A yayin jawabin, Tenebe ya kuma yi amfani da kalmar “AK-47” wajen gargadin waɗanda ya ce suna ƙoƙarin kawo cikas ga shirin jam’iyyar na samun ƙuri’un.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng