Bayan Atiku, an Samu Dan Takarar da ake Ganin zai Kayar da Tinubu a 2027

Bayan Atiku, an Samu Dan Takarar da ake Ganin zai Kayar da Tinubu a 2027

  • Jam’iyyar NDC ta bayyana kwarin gwiwar cewa dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi, zai iya samun gagarumar nasara a zaben 2027.
  • Ta ce hadin gwiwar magoya bayan Obi da tafiyar Kwankwasiyya na iya samar da karfin siyasa da zai kalubalanci APC a Arewa da Kudancin Najeriya
  • NDC ta kuma yi ikirarin cewa matsin tattalin arziki, tsadar rayuwa da matsalar tsaro na iya sa masu kada kuri’a su sauya matsayarsu a zaben mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Jam’iyyar NDC ta bayyana cewa dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi, na da damar lashe zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 16 ga Janairu, 2027.

Jam’iyyar ta ce hadin gwiwar Obi da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, tare da korafe-korafen da ake samu kan halin da kasa ke ciki, na iya taimaka musu wajen samun nasara.

Kara karanta wannan

"Alamu da lissafin siyasa sun nuna wanda zai lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027"

Dan takarar NDC, Peter Obi
Peter Obi da ke yi wa NDC takara. Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto cewa mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben NDC na kasa, Dr Chiogo Constance Ikokwu, ce ta bayyana hakan, inda ta ce jam’iyyar na ganin tana da karfin siyasa da zai iya kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki.

Me za sa Obi cin zabe?

Ikokwu ta ce zaben 2023 ya nuna karfin siyasar Obi a jihohin Arewa ta Tsakiya, inda ya samu nasara a Filato, Nasarawa da Babban Birnin Tarayya Abuja.

Ta kuma yi ikirarin cewa Obi na da goyon baya a Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu, yayin da hadin gwiwarsa da Kwankwaso zai iya kara masa karfi a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.

Ta ce wasu na kuskuren daukar natsuwar Obi a matsayin rauni, alhali tana ganin yana da juriya da karfin fuskantar kalubalen siyasa.

Ikokwu ta kara da cewa magoya bayan Obi da Kwankwasiyya na iya hada karfi wajen samar da babban hadin gwiwar siyasa da zai iya kalubalantar duk wata jam’iyya a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Tinubu ya amince a dauki sababbin sojoji 28000 da ‘yan sanda 50000 aiki

Tasirin Kwankwasiyya a 2027

NDC ta ce tafiyar Kwankwasiyya na daga cikin manyan abubuwan da za su iya taimaka wa Obi samun goyon bayan masu kada kuri’a, musamman a yankin Arewa.

Ikokwu ta bayyana cewa Kwankwasiyya kungiya ce da ta kafu a matakin tushe, kuma tana da tsari da magoya baya da aka gwada a zabuka.

Ta ce:

“Kwankwasiyya ta gina tsari mai karfi na magoya baya a matakin tushe, wanda ya mamaye Kano tare da samun karbuwa a sauran yankunan Arewa. Hada wadannan manyan kungiyoyin magoya baya biyu a karkashin NDC zai iya hada Arewa da Kudu, tare da samar da kawancen siyasa mai karfi.”

Ta kuma yi ikirarin cewa hadin gwiwar Obidient da Kwankwasiyya zai iya zama kalubale ga duk masu kokarin magudin zabe.

Peter Obi da Rabiu Kwankwaso
Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a wajen taron NDC. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Twitter

Matsin tattalin arziki da rashin tsaro

Ikokwu ta bayyana cewa halin tattalin arzikin Najeriya na daga cikin manyan batutuwan da za su iya shafar zaben 2027.

Kara karanta wannan

Dalilan da ake gani za su iya sa Atiku ya yi nasara a kan Tinubu a 2027

Ta yi ikirarin cewa farashin kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabi, inda ta ce buhun shinkafa da a baya ake sayarwa a kusan N15,000 ya haura N70,000.

Ta kuma danganta karuwar farashin man fetur da tsadar sufuri, wahalhalun da kananan ’yan kasuwa ke fuskanta da raguwar kudin shiga na jama'a.

Dangane da bashin Najeriya, mai magana da yawun NDC ta yi ikirarin cewa bashin gwamnati ya haura dala biliyan 120, tana mai tambayar yadda aka yi amfani da kudin da aka ciyo da kuma ribar cire tallafin man fetur.

Ta ce matsalar yunwa da rashin tsaro na iya kara shafar yadda al’ummar Arewa za su kada kuri’a a zaben 2027.

Abubuwan da za su taimaki Atiku

A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na kara kokarin neman goyon bayan al’ummar Arewa gabanin zaben shugaban kasa na 2027.

Tsohon Ministan Wasanni, Solomon Dalung, ya yi ikirarin cewa wasu magoya bayan marigayi Muhammadu Buhari na karkata zuwa Atiku, yayin da rashin gamsuwa kan tsadar rayuwa da matsalar tsaro ke kara zama batun siyasa.

Atiku na da dimbin alaka da magoya baya a Arewa, lamarin da ka iya taimaka masa wajen kalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC a zaben mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng