Mummunar Sauya Sheka Ta Kara Raunana Jam’iyyar NDC da Kwankwasiyya a Jihar Kano
- NDC ta samu matsala a karamar hukumar Bichi ta jihar Kano sun sauya sheka a karkashin jagorancin Haladu Sa’adu
- Mataimakin shugabanta jam’iyyar na ƙaramar hukuma, shugabannin mazabu da wasu jiga-jigan Kwankwasiyya sun koma APC
- Sun kuma zargi NDC a Kano da rashin kyakkyawan tsari da rashin girmama ‘ya ‘ya, don haka suka bi Abubakar Kabir Bichi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - An yi wa jam’iyyar NDC lahani a ƙaramar Hukumar Bichi ta Jihar Kano biyo bayan ficewar wasu shugabannin da manya a Kwankwasiyya.
Mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙaramar hukumar, shugabannin mazabu biyar da wasu jagororin tafiyar Kwankwasiyya sun bi jam’iyyar APC.
Shugabannin NDC a Bichi sun shiga APC
An tarbi waɗanda suka sauya sheƙar ne a ranar Litinin, 16 ga Nuwamba, 2026, a ofishin ɗan majalisar tarayya da ke garin Bichi a cewar Tribune.
Ɗan majalisar kuma shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi ya yi sanadin sauya sheƙar tasu.
Tawagar waɗanda suka sauya sheƙar ta samu jagorancin mataimakin shugaban NDC a Bichi, Haladu Sa’adu.
Wadanda NDC ta rasa zuwa jam'iyyar APC a Kano
Sauran waɗanda ke cikin tawagar sun haɗa da ma’ajiin NDC, Mannir Umar; shugabannin mazabun Waire, Danzabuwa, Kaukau, Muntsira sai kuma Bichi.
Sakatarorin ƙaramar Hukumar Bichi, shugabannin mata da matasa da kuma sauran fitattun mambobin tafiyar Kwankwasiyya duk sun sauya-shekar.
Da yake magana a madadin waɗanda suka sauya sheƙar, shugaban ƙungiyar kuma shugabanta a mazabar Danzabuwa ya ce sun yanke shawarar shiga APC.
Meyasa shugabannin Kwankwasiyya suka bar ta?
Abdulkadir Lawan ya ce sun canza gida saboda abin da ya bayyana a matsayin jajircewar ɗan majalisar tarayyar wajen kawo masu ci gaba a garin Bichi.
Ya ce irin taimakon da ya samu da kansa daga shirin bayar da tallafin karatu na ɗan majalisar ya ba shi damar samun digirin digirgir don haka ya bi APC.
Lawan ya bayyana cewa a halin yanzu yana karatun digiri na uku (PhD) ne ta hannun gidauniyar Abubakar Kabir Foundation ba tare da cin zarafi ba.
Ya kuma bayyana zargin rashin kyakkyawan tsarin gudanarwa da rashin girmama mambobi daga shugabancin NDC a Kano a matsayin dalilin tsallensu.
‘Dan siyasar soki jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda shi ne uba na NDC a jihar.
'Dan majalisa ya yi masu maraba da shigowa APC
Da yake tarbar waɗanda suka sauya sheƙar, Abubakar Kabir Bichi ya yi masu maraba da shiga APC, tare da yaba masu da suka yi na’am da jagorancinsa.
Ɗan majalisar tarayyar ya bayyana wasu daga cikin ayyukan raya ƙasa da ya gudanar a mazabarsa ta Danzabuwa, ciki har da gina makaranta da tituna.
Bichi ya samar da rijiyoyin burtsatse domin inganta samun ruwan sha mai tsafta a mahaifarsa.
Daily Nigerian ta ce ya buƙaci sababbin ‘ya ‘yan da suka shigo jam’iyyar da su haɗa kai da sauran masu ruwa da tsaki a APC domin tabbatar da nasara.
Sauran wadanda aka gani a taron jam'iyyar
Rahoton ya ce taron sauya shekar ya samu halartar ɗan majalisa mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar Dokokin Jihar Kano, Hon. Lawan Shehu Bichi.

Kara karanta wannan
Akume ya ɗauko abin da ya faru a 1999, ya zargi Atiku da yunƙurin karya alƙawari a zaɓen 2027
Sani Mukaddas Bichi, Alhaji Babangida Danzabuwa, Farfesa Yusuf Muhammad Sabo, Alhaji Ahmad Aruwa da sauran shugabannin APC sun halarci taron.
Bichi ya nemi su dage wajen ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran ’yan takarar jam’iyyar duk sun lashe zaben 2027.
Batun auren Gwamnan jihar Kano
An samu rahoto cewa tsohon shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ne ake sa ran zai ceto auren Abba Kabir Yusuf da Zainab Kwankwaso.
Hakan yana zuwa ne bayan an ji cewa diyar tsohon gwamnan ta nemi kotun shari'a ta raba aurensu.
Wannan aure tsakanin Abba Kabir Yusuf da Zainab Kwankwaso ya zarce shekaru 20 kuma Allah ya albarkace shi da 'ya 'ya shida kamar yadda aka ji labari.
Asali: Legit.ng

