Alkawarin da Atiku Abubakar Ya Yi wa Mutane da ADC Ta Je Kamfen ADC a Bauchi

Alkawarin da Atiku Abubakar Ya Yi wa Mutane da ADC Ta Je Kamfen ADC a Bauchi

  • Atiku Abubakar ya sha alwashin ci gaba da aikin hako mai a rijiyar Kolmani da ke tsakanin Bauchi da Gombe ya zama shugaban kasa
  • ‘Dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar ADC ya kuma yi alkawarin dawo da tallafin fetur da wutar lantarki tare da magance matsalar tsaro
  • Alhaji Atiku ya bukaci al'ummar Bauchi su zabi ADC daga sama har kasa, sannan su kare kuri'unsu a babban zaben shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Bauchi - Atiku Abubakar mai takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC ya ce zai tabbatar da ci gaba da aikin hako mai a Arewacin Najeriya.

Gwamnatin Atiku Abubakar za ta dage wajen ganin an samu mai a yankin Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe idan aka zabi ADC.

Atiku
'Dan takaran ADC, Atiku Abubakar tare da Sarkin Misau a jihar Bauchi @Atiku
Source: Twitter

Atiku Abubakar ya tallata ADC a jihar Bauchi

Kara karanta wannan

Tinubu ya leƙo babbar matsalar ƴan Plateau, ya ɗauka masu alƙawari

Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na ADC a jihar Bauchi a cewar The Cable.

A watan Nuwamban 2023, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin Kolmani Integrated Development Project.

Wannan aiki ya hada da hako mai a yankin da ke tsakanin Bauchi da Gombe, sai dai har yanzu ba a fara aikin hakar man yadda aka tsara ba.

Da yake jawabi a wajen gangamin jam’iyyar hamayya ta ADC a garin Bauchi, Atiku ya nanata cewa zai maido tallafin man fetur da na lantarki.

‘Dan adawan yana nan a kan bakarsa cewa fetur zai yi araha idan ya karbi mulki domin za a saida danyen mai ga matatu a kan farashi mai sauki.

"Na riga na yi wa daukacin 'yan Najeriya alkawarin cewa zan dawo da tallafin man fetur.
"Ba wannan kadai ba, zan kuma dawo da tallafin wutar lantarki.
"Na kuma yi alkawarin dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin Arewa maso Gabas da sauran sassan kasar nan. Haka kuma, na yi alkawarin ci gaba da aikin hako man fetur a yankin Kolmani domin samar wa Najeriya wata hanyar samun karin kudaden shiga."

Kara karanta wannan

"Yadda aka dakatar da limamin masallaci saboda ya ja Atiku Abubakar sallah"

- Atiku Abubakar

Kiran Atiku na zaben jam'iyyar ADC a Bauchi

Atiku ya bukaci mazauna jihar Bauchi su zabi 'yan takarar ADC a dukkan mukaman siyasa a 2027.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma bukaci al'ummar jihar su fito kwansu da kwarkwatarsu domin yin zabe sannan su kare kuri’arsu.

Ya ce:

"Ina son ku tabbatar kun fito da yawanku, kun zabi ADC, kun kare kuri'unku, kun tabbatar an kirga kuri'un yadda ya kamata, sannan an aika sakamakon zabe ta hanyar sadarwa kafin ku bar rumfar zabe."

Tashar AIT ta rahoto Atiku yana daukar wadannan alkawari yana kuma mai yaba wa mutanen jihar.

Yake cewa al'ummar Bauchi sun yi fice wajen kare hakkokinsu a tarihin siyasa don haka ya bukace su da su ci gaba da hakan tun daga sama har kasa.

Atiku yana so daga zaben shugaban kasa har zuwa na 'yan majalisar dokokin jiha, a yi kokari wajen ganin nasarar jam’iyyarsu ta ADC a fadin Bauchi.

Kara karanta wannan

'Na yi mamakin abin da Atiku ya yi mini': Nafiu Bala ya yi ɓarin zance

'yan ADC
Tawagar jam'iyyar ADC a fadar Sarkin Misau Hoto: @Atiku
Source: Twitter

Gwamna ya koka da jinkirin aikin hako mai

A baya an ji cewa Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya nuna damuwarsa kan jinkirin fara aikin hako mai a rijiyar Kolmani, yake nuna illar bata lokacin.

Inuwa Yahaya ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa, bayan nan an ji cewa za a tado da zancen aikin.

Idan har an yi nasarar hako mai, za a sa jihohin Arewa cikin masu arzikin danyen mai a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng