Gwamna Zulum Ya Umarci Cafke 'Yan 'Tinubu Must Go' a Borno? An Ji Yadda Zancen Yake

Gwamna Zulum Ya Umarci Cafke 'Yan 'Tinubu Must Go' a Borno? An Ji Yadda Zancen Yake

  • Gwamna Zulum ya yi watsi da sanarwar ADC kan zargin cewa ya yi barazanar kama masu sanya riga mai rubutun “Tinubu Must Go”
  • Kakakin gwamnan ya ce ADC ta dogara ne da rahoton da bai dace da ƙa’idojin aikin jarida ba wajen yin zargin
  • Gwamnatin Borno ta ce jawabin Zulum ya shafi tsaro da yaƙi da miyagun laifuffuka ne, ba jam’iyyar ADC ko wata ƙungiyar adawa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi martani kan zargin da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban kasa na ADC na bayar da umarnin cafke 'yan adawa.

Gwamnan ya ce sanarwar ba ta da ingantaccen tsari, kuma siyasa ce ta matsa wa jam’iyyar lamba ta fitar da ita.

Zulum ya musanta umarnin cafke 'yan adawa
Gwamna Babagana Umara Zulum na jawabi a wajen taro Hoto: Dauda Iliya
Source: Facebook

ADC ta soki Zulum kan bidiyon “Tinubu Must Go”

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya aika sako ga masu rike da mukamai bayan fara guna guni

Jaridar Daily Trust ta ce a ranar Lahadi, 4 ga watan Oktoban 2026, Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na ADC ya soki Gwamna Zulum kan wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta.

A cikin bidiyon, ana zargin gwamnan da bayar da umarnin kama da tsare duk wanda aka samu yana bayyana kalmar “Tinubu Must Go”.

ADC ta bayyana hakan a matsayin tsauraran matakan da ake amfani da su wajen dakile ’yancin faɗin albarkacin baki da kuma murƙushe masu adawa da gwamnati.

Gwamnan ya ce ADC ta karkatar da bayanansa

A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Dauda Iliya, ya fitar a shafinsa na Facebook, ya bayyana zargin ADC a matsayin wanda bai dace da ƙa’idojin aikin jarida ba.

Ya ce jam’iyyar ta karkatar da abin da Gwamna Zulum ya faɗa a wani taron manema labarai da ya gudanar a Maiduguri.

“Mun karanta cikin takaici sanarwar baya-bayan nan da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na ADC ya fitar, wadda ta yi kalaman gaggawa kan gwamnatin Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum,” in ji sanarwar.

Ya ƙara da cewa sanarwar jam’iyyar ba a yi ta cikin zurfin tunani ba, kuma sakamakon matsananciyar buƙatar siyasa ce.

Kara karanta wannan

Malamar addini ta fito ta gayawa Tinubu gaskiya kan halin da ake ciki a Najeriya

Gwamnati ta ce batun tsaro Zulum ya tattauna

A cewar kakakin gwamnan, Zulum ya gana da manema labarai ne domin tattauna wasu batutuwan da suka shafi jihar, ciki har da ƙaruwa da aka samu a wasu munanan halaye da laifuffukan da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron Borno.

Ya ce gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta zauna tana kallon matasa da ’yan daba ko masu aikata laifuffuka suna jefa jihar cikin rikici ba.

An ce Zulum ya yi magana ne kan wasu matasa da ke yawo sanye da riguna masu ɗauke da hotunan wuƙaƙe da sanduna, abin da gwamnati ta ce yana ƙarfafa al’adar tashin hankali.

An kafa rundunar yaƙi da miyagun halaye

Sanarwar ta ce bayan tashe-tashen hankulan Boko Haram, jihar Borno ta fuskanci ƙaruwa a wasu matsalolin zamantakewa, ciki har da daba, satar ƙananan ’yan mata, zubar da ciki ba bisa ƙa’ida ba, satar wayoyin hannu da sauran laifuffuka.

Kara karanta wannan

Amaechi ya hango barazanar da ke fuskantar 'yan adawa idan Tinubu ya zarce a 2027

Saboda haka, gwamnatin jihar ta kafa wata rundunar tsaro ta musamman da ke yaƙi da waɗannan miyagun halaye.

A cewar gwamnatin, tun bayan fara ayyukan rundunar, Maiduguri da kewayenta sun samu ƙarin tsaro, yayin da aka samu raguwar laifuka da sauran munanan halaye.

Gwamnatin Borno ta ce ADC ba ta cikin jawabin Zulum

Dauda Iliya ya zargi wasu kafafen yaɗa labarai da yin watsi da ƙa’idojin aikin jarida, yana mai cewa sun ɗauki wani ɓangare na bayanin Zulum suka gina labari da nufin nuna gwamnan a matsayin mai tsaurin mataki.

Ya ce Zulum bai ambaci ƙungiyar “Tinubu Must Go”, ADC ko wata ƙungiyar adawa ba a yayin ganawarsa da manema labarai.

“Gwamna Zulum bai taɓa ambaton ƙungiyar #TinubuMustGo, ADC ko wata ƙungiyar adawa ba. Ya yi magana ne kawai kan tsaro, zaman lafiya da bin doka da oda,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa sanarwar ADC na iya zama kamar ta ɗauki alhakin laifuffukan da ake zargin wasu daga cikin waɗannan ƙungiyoyi suna aikatawa a jihar.

Kara karanta wannan

Oshiomhole ya fallasa abin da Atiku ya gaya masa kan tallafin man fetur

Gwamna Zulum ya yi wa ADC martani
Gwamna Zulum na jawabi a wajen taron gwamnonin Arewa maso Gabas Hoto: Dauda Iliya
Source: Facebook

Zulum ya yi maganar tsarin rabon mulki

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi magana kan tsarin rabon mulki tsakanin Arewa da Kudancin Najeriya da kuma zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Gwamna Zulum ya ce shugabannin Arewa sun yanke shawarar mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a ƙoƙarinsa na neman wa’adi na biyu, da fahimtar cewa mulki zai koma Arewa bayan ya kammala wa’adinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng