Jerin Yan Najeriya 4 da Suka Lashe Kujeru Daban Daban a Zaben Amurka, na 5 na Hanya
’Yan Najeriya huɗu da ke zaune a Amurka sun lashe zaɓen kujerun siyasa daban-daban a ƙasar, yayin da wani na biyar ke kan gaba a zaɓen da ake sa ido sosai a kai a Jihar Georgia.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Yan Najeriya sun samu wannan nasara ne a zaɓen tsakiyar wa’adi da aka gudanar a ranar 3 ga Nuwamba, 2026, wan da jam'iyyar Shugaba Donald Trump ta rasa rinjaye a Majalisa.

Source: Facebook
Daily Trust ta ce waɗannan nasarori, waɗanda aka samu a Maryland, Texas, Washington DC da Pennsylvania, sun nuna yadda ’yan Najeriya da waɗanda iyayensu ’yan Najeriya ne ke ƙara shiga harkokin siyasa da samun wakilci a siyasar Amurka.
Waɗanda suka yi nasarar sun haɗa da Will Jawando, Junior Ezeonu, Oye Owolewa da Carol Kazeem, waɗanda suka samu muƙamai a majalisun dokokin ƙananan hukumomi da jihohi, da kuma Majalisar Gundumar Columbia.
Wani ɗan siyasa kuma ɗan asalin Najeriya, Segun Adeyina, na kan gaba a ƙoƙarinsa na riƙe kujerarsa a Majalisar Dokokin Jihar Georgia, duk da cewa ba a kammala sanar da wanda ya lashe zaɓen ba yayin da ake ci gaba da ƙirga ƙuri’u.
1. Jawando ya lashe zaɓen Maryland
A Jihar Maryland, ɗan jam’iyyar Democrat, Will Jawando, ya doke ’yar jam’iyyar Republican, Esther Wells, inda ya zama sabon shugaban gundumar Montgomery.
Jawando, wanda mahaifinsa ɗan Najeriya ne, mahaifiyarsa kuma Ba’amurkiya ce, ya taɓa zama ɗaya daga cikin wakilan Majalisar Montgomery. An fara zaɓensa a shekarar 2018.

Source: Facebook
Sakamakon zaɓen da ba a kammala tabbatarwa a hukumance ba, wanda Moderately MOCO ta wallafa, ya nuna cewa Jawando ya samu ƙuri’u 195,872, kwatankwacin kashi 78.66%, yayin da Wells ta samu ƙuri’u 52,141, wato kashi 20.94%, zuwa ƙarshen ranar Talata.
Jawando zai gaji Marc Elrich, wanda ke barin muƙamin bayan ya shafe wa’adi biyu yana jagorantar gundumar.

Kara karanta wannan
Nasara daga Allah: Dakarun sojojin Najeriya sun tura yan ta'adda sama da 200 lahira
2. Ezeonu ya lashe kujerar Texas
A Jihar Texas, ɗan jam’iyyar Democrat mai shekara 27, Junior Ezeonu, ya lashe zaɓen kujerar mazaba ta 101 a Majalisar Wakilan Jihar.
An haifi Ezeonu a Onitsha, Jihar Anambra, amma ya koma Texas tare da iyalinsa yana ɗan shekara biyu.
Ya doke mai riƙe da kujerar, Chris Turner, a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar Democrat a watan Maris na 2026.

Source: Facebook
Daga bisani, ya zama shi kaɗai ne ɗan takara a babban zaɓen watan Nuwamba bayan babu ɗan jam’iyyar Republican da ya shiga takarar.
Sakamakon da shafin bibiyar sakamakon zaɓen Texas ya wallafa ya nuna cewa Ezeonu ya samu ƙuri’u 37,278 a zaɓen da babu abokin hamayya.
3.Owolewa ya samu kujera a Washington DC
A Washington DC, ɗan jam’iyyar Democrat, Oye Owolewa, ya lashe kujerar wakilin gundumar baki ɗaya a Majalisar Gundumar Columbia.
Owolewa, wanda ma’aikacin harhaɗa magunguna ne, ɗa ne ga ’yan Najeriya da suka yi ƙaura daga jihohin Kwara da Osun zuwa Amurka.

Source: Facebook
A baya, ya yi aiki a matsayin zaɓaɓɓen wakili na gundumar, muƙamin da aka samar domin fafutukar ganin Washington DC ta zama jiha tare da samun cikakken wakilci a Majalisar Dokokin Amurka.
4. Kazeem ta riƙe kujerarta a Pennsylvania
A Jihar Pennsylvania, ’yar jam’iyyar Democrat, Carol Kazeem, ta sake lashe zaɓen kujerar da take wakilta ta mazabar 159 a Majalisar Wakilan Jihar.
Kazeem ta doke abokin takararta na jam’iyyar Republican, Mike Bannon, bisa ga sakamakon farko da aka fitar. Sakamakon ya nuna cewa Kazeem ta samu ƙuri’u 12,801, yayin da Bannon ya samu 4,109.
Tana cikin ’yan Najeriya takwas da suka lashe kujerun majalisun dokoki a zaɓen tsakiyar wa’adi na Amurka na shekarar 2022.

Source: Facebook
5. Adeyina na kan gaba a Georgia
A halin da ake ciki, ɗan jam’iyyar Democrat da aka haifa a Najeriya, Segun Adeyina, na kan gaba a takarar kujerar mazabar 110 ta Majalisar Wakilan Jihar Georgia, inda yake fafatawa da ɗan jam’iyyar Republican, Charles Lollar.
Bisa ga bayanan shafin bibiyar sakamakon zaɓe, Adeyina ya samu ƙuri’u 1,353, yayin da Lollar ya samu 689, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Wannan ya ba Adeyina kashi 66% na ƙuri’un da aka ƙirga, yayin da Lollar ya samu kashi 34%, a lokacin da aka ƙiyasta cewa an ƙirga kashi 8% na ƙuri’un da ake sa ran za a kaɗa.
Adeyina, wanda ke wakiltar wasu sassan gundumar Gwinnett, ya fara samun kujerar Majalisar Dokokin Jihar Georgia ne a shekarar 2022.
Duk da cewa ba a sanar da wanda ya lashe zaɓen a hukumance ba, daga baya bayanan bibiyar zaɓen sun nuna cewa Adeyina ne ya yi nasara.
Musulmi ya kafa tarihi a Amurka
Kun ji cewa Abdul El-Sayed, ɗan jam'iyyar Democrat, ya lashe zaɓen sanatan Amurka a jihar Michigan bayan doke ɗan takarar Republican, Mike Rogers.
El-Sayed, wanda aka haifa a jihar Michigan ga iyayensa 'yan gudun hijira daga Masar, ya kafa tarihi a matsayin Musulmi na farko da aka zaɓa a matsayin sanatan Amurka.
Asali: Legit.ng


