Yadda Iran Ta 'Jawo wa' Trump Faduwa Zabe a Amurka, Ya Ce Ya Yi Mamaki

Yadda Iran Ta 'Jawo wa' Trump Faduwa Zabe a Amurka, Ya Ce Ya Yi Mamaki

  • Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce yaƙin da ƙasarsa ta shiga da Iran na daga cikin dalilan da suka janyo wa jam'iyyar Republican rashin nasara a zaɓe
  • Trump ya bayyana cewa ya yi mamakin sakamakon zaɓen, domin yana tunanin 'yan takarar jam'iyyarsa za su samu nasara fiye da haka
  • Sai dai ya ce duk da asarar da jam'iyyarsa ta yi, yaƙin Iran zai fi muhimmanci a tarihi saboda ba za a bar ƙasar ta mallaki makamin nukiliya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya amince cewa yaƙin da ƙasarsa ta shiga da Iran ya taimaka wajen janyo wa jam'iyyar Republican faduwa a zaɓen tsakiyar wa'adin mulkin Amurka.

Trump ya bayyana hakan ne ranar Laraba, yayin da jam'iyyar Democrat ta karɓe ikon Majalisar Dokokin Amurka, lamarin da ya zama babban koma-baya ga shugaban ƙasar.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar Trump ta sha kaye a zaben Amurka, abin da yake tsoro ya faru

Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump na sauraron wani jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cewar rahoton Reuters, duk da tasirin yaƙin kan sakamakon zaɓen, yana ganin matakin da ya ɗauka kan Iran zai fi muhimmanci a tarihi.

Abin da Donald Trump ya ce kan yaƙin Iran

Yayin da yake bayani kan sakamakon zaben, Trump ya ce:

“Ina ganin yaƙin Iran na daga cikin dalilan, amma a lokaci guda, mutane sun fahimci muhimmancin abin da na yi game da Iran. A tarihi, wannan zai fi abin da ya faru a wannan daren muhimmanci, domin ba za a iya barin ƙasar da ta fi kowace ƙasa ɗaukar nauyin ta'addanci ta mallaki makamin nukiliya ba.”

Kafin zaɓen, batun yaƙin Iran ya zama babban abin tattaunawa a tsakanin Amurkawa, inda da dama suka bayyana cewa bai kamata Amurka ta shiga hare-haren da Isra'ila ta kai wa Iran ba.

Haka kuma, tashin farashin man fetur bayan fara rikicin ya ƙara jawo rashin gamsuwa, har ma a tsakanin wasu magoya bayan Trump, ciki har da Tucker Carlson, wanda ya fito ya soki matakin shugaban ƙasar.

Kara karanta wannan

Iran ta rataye hoton barazanar kashe Donald Trump a Tehran

Trump ya sha mamakin zaɓen Amurka

Shugaban Amurka ya kuma bayyana mamakinsa kan yadda jam'iyyarsa ta gaza samun cikakken sakamako da ta yi buri a zaɓen.

A wata hira da gidan talabijin na Fox News, Trump ya ce ya yi tsammanin 'yan takarar Republican za su fi samun nasara.

A cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na AP, a lokacin da aka fitar da rahoton, jam'iyyar Democrat ta samu kujeru 52 a Majalisar Dattawa, yayin da take kan hanyar karɓe ikon Majalisar Wakilan Amurka.

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sai dai Trump ya bayyana cewa da shi ne aka saka a cikin jerin 'yan takarar, da jam'iyyarsa ta samu gagarumar nasara.

A wani saƙo da ya wallafa a ranar Talata da dare, ya ce:

“Ba a saka sunana a cikin takardar zaɓe ba, da a ce an saka, da mun yi nasara da gagarumin rinjaye.”

Duk da rashin nasarar jam'iyyarsa, Trump ya bayyana cewa a shirye yake ya yi aiki tare da 'yan jam'iyyar Democrat bayan sun samu rinjaye a majalisun dokokin ƙasar.

Kara karanta wannan

Mutanen Tinubu sun fita daga APC sun koma wajen Atiku a ADC

Ilhan Omar ta sake lashe zaben majalisa

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yar majalisar wakilan Amurka, Ilhan Omar, ta sake lashe zaɓe domin ci gaba da wakiltar gundumar Minnesota ta 5.

Nasarar Omar ta zo ne a daidai lokacin da Shugaba Donald Trump ke ci gaba da kai mata hare-hare, inda ya nemi ta yi murabus daga majalisa.

Trump ya sake tayar da zargin ne bayan wani takardar shari'a ya ambaci wata ƙarin suna da ake dangantawa da 'yar siyasar ta Minnesota.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng