Obi Ya Fadi Yadda zai Yi Aiki Tare da Kwankwaso idan Suka Yi Nasara a 2027

Obi Ya Fadi Yadda zai Yi Aiki Tare da Kwankwaso idan Suka Yi Nasara a 2027

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, ya yi alkawarin yin aiki kafada da kafada da abokin takararsa, Rabiu Kwankwaso idan suka lashe zaɓen 2027
  • Obi ya ce gwamnatinsa za ta ba da fifiko ga tsaro da ilimi, tare da ayyana dokar ta-ɓaci a ɓangaren ilimi domin magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta
  • Kwankwaso ya buƙaci ’yan Najeriya su haɗa kai, su fita kaɗa ƙuri’a tare da kare ƙuri’unsu, yayin da Sanata Victor Umeh ya bayyana tikitin Obi-Kwankwaso a matsayin mafi dacewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Enugu – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya sake jaddada aniyarsa ta yin aiki tare da abokin takararsa na mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Masu shirin magudin zabe sun shiga uku, Peter Obi ya yi masu barazana ga INEC

Obi ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin wani taron tattaunawa da jama’a a Enugu, inda ya yi musayar ra’ayi da magoya bayansa da sauran masu ruwa da tsaki kan matsalolin ƙasar da kuma manufofinsa na ci gaba.

Peter Obi tare da Rabiu Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso da Peter Obi a wajen taron NDC. Hoto: Raiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Obi zai yi aiki da Kwankwaso

Vanguard ta rahoto cewa tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce shi da Kwankwaso za su yi aiki tare domin magance matsalar rashin tsaro da dawo da zaman lafiya a faɗin Najeriya idan aka zaɓe su a shekarar 2027.

Ya ce kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya zai kasance cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa za ta ba fifiko, tare da ɗaukar matakan magance matsalolin tsaro da ke barazana ga al’ummomi da hanyoyin samun abin dogaro da kai.

Obi ya nuna damuwa kan yadda ya ce gwamnatin da ke mulki a yanzu ta gaza wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya, duk da cewa wannan na daga cikin manyan nauyin da ke wuyan gwamnati.

Ya kuma buƙaci masu zaɓe a Kudu maso Gabashin Najeriya su mara masa baya, yana mai cewa yana da ƙwarewa da damar tunkarar matsalolin da ƙasar ke fuskanta.

Obi zai inganta ilimi

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya bude sabon shafi a TikTok, ya bayyana irin bidiyoyin da zai fara wallafawa

A yayin taron, Obi ya ce zai ayyana dokar ta-ɓaci a fannin ilimi idan ya zama shugaban ƙasa, domin magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta.

Ya jaddada cewa yaran Najeriya sun cancanci samun ingantaccen ilimi, yana mai cewa gwamnatinsa za ta ɗauki matakan da suka dace domin fuskantar matsalolin da ke hana yara samun ilimi.

Ɗan takarar ya kuma ƙalubalanci sauran ’yan takarar shugaban ƙasa da su fito su tattauna manufofinsu da yadda za su magance matsalolin ƙasar.

Bayanin Rabiu Kwankwaso

A nasa jawabin, abokin takarar Obi na mataimakin shugaban ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya gargaɗi ’yan Najeriya da kada su bari siyasar ƙabila ta ruɗe su.

Kwankwaso ya ce:

“A bayyane yake cewa ’yan Najeriya suna fuskantar matsaloli masu yawa.”

Ya lissafa matsalolin da suka haɗa da rashin tsaro, rashin aikin yi, talauci da yunwa, yana mai cewa waɗannan matsaloli na ƙara wa al’umma wahala.

Manyan NDC a Najeriya
Peter Obi da manyan NDC a wajen taro. Hoto: MR Peter Obi
Source: Facebook

A cewarsa, hanyar cimma sabuwar Najeriya ita ce haɗin kai, jajircewa, haƙuri da kuma niyyar yin aiki domin kawo sauyi.

Ya buƙaci ’yan Najeriya su fito da yawa domin kaɗa ƙuri’unsu, su kare su tare da bibiyar yadda ake ƙirga ƙuri’u har sai an sanar da sakamako.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ceto mutane 70, sun kama ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi mutane a Arewa

ADC ta gayyaci Atiku

A wani labarin, kun ji cewa daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na NDC, Ibrahim Abdulkarim, ya yi kira ga Atiku Abubakar ya hada kai da Obi.

Ibrahim Abdulkarim ya ce haɗin kan ’yan adawa a ƙarƙashin dandali guda zai ƙara musu damar kayar da jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen.

Ya bayyana cewa ba lallai ne haɗin kan ’yan adawa ya gudana a ƙarƙashin jam’iyyar ADC ba, domin za a iya yin hakan a ƙarƙashin NDC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng