Jam'iyyar Trump Ta Sha Kaye a zaben Amurka, Abin da Yake Tsoro Ya Faru

Jam'iyyar Trump Ta Sha Kaye a zaben Amurka, Abin da Yake Tsoro Ya Faru

  • Jam'iyyar Democrat ta samu rinjaye a Majalisar Wakilan Amurka, lamarin da zai kawo ƙarshen ikon jam'iyyar Republican ta Donald Trump
  • Ana sa ran shugaban Democrat, Hakeem Jeffries, zai zama Bakar fata na farko da zai riƙe kujerar shugaban majalisar dokokin Amurka
  • Haka kuma, Amy Acton ta lashe zaɓen gwamnan Ohio, inda ta zama mace ta farko da ta taɓa riƙe wannan muƙami a tarihin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Jam'iyyar Democrat ta samu nasarar karɓe ikon Majalisar Wakilan Amurka daga hannun jam'iyyar Republican ta Donald Trump a zaɓen tsakiyar wa'adin mulkin ƙasar na ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba, 2026.

An yi hasashen haka ne yayin da 'yan jam'iyyar Democrat ke cigaba da lashe kujerun majalisa yayin da sakamakon zabe ke bayyana.

Kara karanta wannan

Iran ta rataye hoton barazanar kashe Donald Trump a Tehran

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gidan talabijin na CNN ya ce sakamakon hasashen cibiyar tantance zaɓensa ya nuna Democrat za ta samu rinjaye a majalisar, lamarin da zai buɗe sabon babi na takun-saka tsakanin 'yan majalisa da Shugaba Donald Trump.

Wani rahoto da Al Jazeera ta wallafa a X ya nuna cewa Democrat ta samu kujeru 51 a majalisar dattawan Amurka, lamarin da ya ba ta damar samun rinjaye.

Hakeem Jeffries zai yi nasara

Bayan nasarar jam'iyyar Democrat, ana sa ran shugabanta, Hakeem Jeffries, zai zama sabon shugaban Majalisar Wakilan Amurka.

Idan hakan ta tabbata, Jeffries zai zama Bakar fata na farko da ya taɓa riƙe wannan muƙami a tarihin Amurka.

Nasarar Democrat ta kawo ƙarshen rinjayen jam'iyyar Republican a majalisar, inda ake sa ran hakan zai ƙara fuskantar da gwamnatin Trump da ƙalubalen siyasa wajen gudanar da ayyukanta.

Democrat ta ƙwace kujerun majalisa

CNN ta kuma yi hasashen cewa jam'iyyar Democrat ta samu nasarar ƙwace kujerun majalisar dattawa guda biyu, ciki har da kujerar jihar South Carolina.

Kara karanta wannan

Mutanen Tinubu sun fita daga APC sun koma wajen Atiku a ADC

A jihar, Annie Andrews ta doke Sanata Darline Graham, yayin da Democrat ke kan gaba a wasu zaɓukan kujerun majalisar dattawa da ake fafatawa a kansu.

Wannan sakamako na zuwa ne a matsayin babban koma-baya ga Trump da jam'iyyar Republican, duk da cewa ana ci gaba da sa ido kan sauran sakamakon zaɓukan.

Majalisar Amurka
'Yan majalisar Amurka na tattaunawa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Amy Acton ta zama gwamna

A wani babban sauyi da aka samu a zaɓen, 'yar jam'iyyar Democrat, Amy Acton, ta lashe zaɓen gwamnan jihar Ohio bayan ta doke ɗan takarar jam'iyyar Republican, Vivek Ramaswamy.

An tabbatar da nasarar ne ta hanyar cibiyar CNN ta tantance zaɓe, inda ta bayyana cewa Acton za ta zama mace ta farko da ta taɓa zama zaɓaɓɓiyar gwamnar Ohio.

Haka kuma, ita ce 'yar Democrat ta farko da ta lashe zaɓen gwamnan jihar tun shekarar 2006. Za ta maye gurbin gwamna mai barin gado, Mike DeWine, wanda dokar wa'adin mulki ba ta ba shi damar sake tsayawa takara ba.

Iran ta gargadi Trump

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Iran ta ƙaddamar da wani babban allo a birnin Tehran mai ɗauke da saƙon barazanar kashe Shugaban Amurka, Donald Trump.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun sha kudi, Tinubu ya raba sama da Naira biliyan 100

Hoton ya nuna Trump a bayan gidan yari, yayin da wasu hotuna suka nuna shi da mataimakinsa da wasu jami'an Amurka da Isra'ila cikin jini.

Masu zanga-zanga sun taru a dandalin Enghelab suna ɗaga tutoci ja tare da neman ɗaukar fansar kisan tsohon jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng